Zargin gwamna da shugabantar Boko Haram: Lauya Bukarti ya shawarci NPF da DSS

Zargin gwamna da shugabantar Boko Haram: Lauya Bukarti ya shawarci NPF da DSS

Fitaccen lauyan nan mazaunin jihar Kano, Barista Bulama Bukarti, ya shawarci rundunar tsaro ta farin kaya da rundunar 'yan sandan Najeriya a kan su binciki zargin cewa daya daga cikin gwamnonin arewa ne ke shugabantar kungiyar Boko Haram.

A ranar Litinin ne kafafen yada labarai su ka wallafa labarin cewa tsohon mataimakin gwamnan babban bankin kasa (CBN), Ubadiah Mailafia, ya yi zargin cewa daya daga cikin gwamnonin arewa ne babban kwamandan kungiyar Boko Haram.

Mailafiya ya bayyana cewa wani tubabben kwamandan kungiyar Boko Haram ne ya sanar da shi hakan.

Da ya ke tsokaci a kan wannan zargi na Mailafia, Bukarti ya bayyana cewa akwai bukatar a binciki wannan zargi domin bai kamata a dauki maganar da wasa ba

"Ina ganin ya kamata rundunar 'yan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) su yi amfani da wannan bayani wajen tatsar karin bayanai daga wurin Mailafia a kan zargin da ya yi.

"Matukar sun tabbatar da gaskiyar zargin da ya yi, ya kamata su tona asirin wannan gwamna, sannan a tsige shi, a gurfanar da shi a gaban kotu.

Zargin gwamna da shugabantar Boko Haram: Lauya Bukarti ya shawarci NPF da DSS
Obadiah Mailafia
Asali: UGC

"Idan kuma Mailafia ya yi zargin ne babu tushe, shi ma ya kamata a hukunta shi. Amma, bai kamata a yi watsi da zargi mai nauyi kamar wannan ba," a cewar Bukarti, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na tuwita.

DUBA WANNAN: N-Power: An bayyana mataki na gaba bayan fiye da mutum miliyan 5 sun nemi aikin

Lauyan ya cigaba da cewa; "matukar Mailafia gaskiya ya fada, bayanansa za su taimaka sosai wajen yaki da kungiyar Boko Haram da ma su daukan nauyin kungiyar.

"Idan kuma karya ya tsara, kalamansa za su kasance ma su hatsari ga tsaron kasa da zaman lafiya a tsakanin kabilun Najeriya, musamman idan aka yi la'akari da zaman doya da manja da ake yi a tsakanin sassan kasa.

Legit.ng ta wallafa rahoton cewa hukumar tsaron farin kaya DSS ta gayyaci Mailafia ranar Talata, kwanaki biyu bayan faifan bidiyon furucin da ya yi ya yadu a dandalin sada zumunta.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa an gayyaceshi ne a kan jawabin da yayi inda ya bayyana cewa daya daga cikin tubabbun yan Boko Haram da aka saki ya fada masa cewa wani gwamnan Arewa ne shugaban kungiyar Boko Haram.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel