Matar aure: Duk tunanina Ma’aikacin jirgi na aura, ban san aikin bola ya ke yi ba

Matar aure: Duk tunanina Ma’aikacin jirgi na aura, ban san aikin bola ya ke yi ba

- A tunanin Shamim, mijinta ma’aikaci ne a filin jirgin sama na Jomo Kenyatta

- Sai kwatsam ta samu labari daga makwabta maigidanta tsintar bola ya ke yi

- Wannan ya yi sanadiyyar da Shamim ta rabu da mutumin da su ka dade tare

Wata Baiwar Allah da ke yankin Embakasi ta rabu da mijinta bayan tsawon shekaru su na zaman aure a sakamakon kama shi da ta yi da laifin yaudara.

Shamin ta shafe shekaru kimanin goma tare da maigidanta, ta na zaton ya na aiki ne a babban filin tashi da saukar jiragen sama na Jomo Kenyatta a kasar Kenya.

A wata hira da ta yi da Anthony Ndiema a filin Nisamehe a wata tashar talabijin a kasar Kenya, Shamim ta ce sai daga baya ta samu labarin inda mijinta ya ke aiki.

Abin takaicin shi ne makwabta ne su ka fasa kwan inda David ya ke aiki bayan wata takaddama ta shiga tsakaninsu da matar da ta ke tunanin ta na auren ma’aikacin filin jirgi.

Wannan mata da yanzu auren ta ya mutu ta ce makwabtanta sun mata izgin cewa ta na auren mutumin da bai da sana’ar da ta wuce roron kayan bola a gari.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun y ram da mai damfarar jama'a da sunan Hadimin Buhari

Matar aure: Duk tunanina Ma’aikacin jirgi na aura, ban san aikin bola ya ke yi ba
Shamim a gidan talabijin Hoto: Youtube
Asali: Facebook

Da Shamim ta rutsa David, sai ya fito mata a mutum, ya tabbatar mata da cewa babu shakka ya boye mata gaskiyar inda ya ke aiki, abin da ba ta taba kawowa a rai ba.

Bayan wannan abu ya faru, David ya ruga gida ya na lallabar matar da su ka dade tare domin ta dawo su cigaba da zaman aure, amma ta watsa masa kasa a idanu.

Miss Shamim ta ce ba ta da niyyar yafewa tsohon mijinta, akalla nan kusa. Ta ce ba ta ga dalilin zama da mutumin da ya boye inda ya ke aiki har na tsawon shekaru goma ba.

Ta ke cewa: “Duk safiya zai yi shiga ta mutunci tsaf, ba za ka taba ganewa ba. Mu na fada da wata a kan ruwa sai ta fada mani cewa mijina yawon roron bola ya ke yi.”

David ya zo gidan talabijin ya bada hakuri, ya ce ya boye gaskiya ne domin gyara miyar soyayya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng