'Ta'addanci ne': Cacar baki ta kaure a kan hukuncin kashe matashi saboda batanci ga Annabi

'Ta'addanci ne': Cacar baki ta kaure a kan hukuncin kashe matashi saboda batanci ga Annabi

Wasu 'yan Najeriya sun mamaye dandalin sada zumunta domin bayyana ra'ayinsu da nuna fushinsu a kan hukuncin kisa da wata kotun shari'ar Musulunci ta zartar a kan wani matashin mawaki.

A ranar Litinin ne wata babbar kotun Shari'a da ke zamanta a Hausawa Filin Hockey da ke cikin birnin Kano ta zartar da hukuncin kisa a kan matashin mai shekaru 22 saboda wallafa wata waka mai dauke da kalaman batanci ga Annabi Muhammad.

Daily Ngerian ta wallafa cewar wata jaridar yanar gizo mai suna 'Focus' da ke Kano ta bayyana cewa alkalin kotun, Khadi Aliyu Muhammad, ya zartar da hukuci a kan matashin, Yahaya Aminu Sharif, da safiyar ranar Litinin.

Jaridar ta bayyana cewa Khadi Muhammad ya zartar da wannan hukunci ne bayan ya gamsu da hujjojin cewa matashin ya aikata laifin da ya jawo aka gurfanar da shi a gaban kotun.

An zargi mawakin da daukaka shugaban darikar Tijaniya a kan Annabi Muhammad - lamarin da ya fusata jama'ar birnin Kano har su ka yi zanga-zanga.

Duk da matashin bai musanta tuhumar da ake yi ma sa ba, Khadi Muhammad ya ce mawakin Yahaya zai iya daukaka kara.

Batun hukuncin kisan ya jawo barkewar cece kuce da musayar yawu a tsakanin 'yan Najeriya a dandalin sada zumunta, musamman shafin manhajar Tuwita.

'Ta'addanci ne': Cacar baki ta kaure a kan hukuncin kashe matashi saboda batanci ga Annabi
'Ta'addanci ne': Cacar baki ta kaure a kan hukuncin kashe matashi saboda batanci ga Annabi
Asali: UGC

Wani ma'abocin amfani da dandalin Tuwita ya bayyana cewa; "babu wurin da aka ambaci irin wannan hukucni a ciki Qur'ani da Hadisai, a saboda haka ba shari'ar Musulunci ba ce.

"zartar da hukuncin kisa saboda batanci bashi da banbanci daga kisan jama'a da sunan 'arna'. Kisa saboda batanci bashi da maraba da ta'addanci."

DUBA WANNAN: JAMB ta sanar da ranar fara jarrabawoyin POST UTME

Shi kuwa wani mazaunin Kano mai suna Khalil cewa ya yi; "babu wanda za a kashe saboda batanci a Najeriya, sai wanda ya ga dama. Shari'ar Musulunci ba ta da gurbi a kasa kamar Najeriya wacce ke amfani da kundin tsarin mulki da ba ruwansa da addini.

Shi kuwa wani ma'abocin amfani da dandalin Tuwita cewa ya yi; "babu wanda ya kamata a kashe saboda wani furuci, a saboda haka zartar da wannan hukcuci ya nuna cewa har yanzu babu cigaba a kasar nan.

"Zartar da hukuncin kisa saboda batanci tamkar take hakkin bil'adama ne, ya zama dole gwamnatin tarayya ta hana kaddamar da wannan hukunci," a cewarsa

Ga wasu daga cikin ra'ayoyin jama'a dangane da hukuncin kotun:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel