Dalla-dalla: Yadda mawaki a Kano ya samu hukuncin kisa saboda batanci ga Annabi

Dalla-dalla: Yadda mawaki a Kano ya samu hukuncin kisa saboda batanci ga Annabi

A jiya Litinin ne wata kotun shari'a ta yankewa matashin mawaki mai shekaru 30 hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon batanci da yayi ga Annabi Muhammadu SAW.

Kotun da ke zama a Hausawa Filin Hockey wacce ta samu shugabancin Khadi Muhammad Ali Kani, ya yanke hukuncin bayan kama Sharif dumu-dumu da laifi.

Duk da cewar 'yan jarida kadan da jami'an tsaro aka bari suka shiga kotun, Daily Trust ta gano cewa laifin ya kusan suma bayan da alkalin ya yanke hukuncin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an saka jami'an tsaro birjik a farfajiyar kotun.

An gurfanar da wanda ake zargin ne a kan batanci ga Annabi, wanda ya ci karo da sashi na 382, sakin layi na 6.

Dalla-dalla: Yadda mawaki a Kano ya samu hukuncin kisa saboda batanci ga Annabi
Dalla-dalla: Yadda mawaki a Kano ya samu hukuncin kisa saboda batanci ga Annabi Hoto: Thisday
Asali: Twitter

Kamar yadda bayanin da maiyarmu ta gano, wanda aka kaman ya yi wallafar ne a manhajar WhatsApp a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2020 inda ya kira Annabi da Mushrik.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sifeta Aminu Yargoje, ya sanar da kotun cewa an yi wannan wallafar ne don saka wani nau'in rashin jin dadi a tsakanin Musulmin jihar.

KU KARANTA KUMA: Kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin INEC, ta dawo da jam'iyyun siyasa 23, za a dangana kotun koli

Kamar yadda takardar ta bayyana, "a ranar 28 ga watan Fabrairu tsakanin karfe 8:00 zuwa 11:00 na dare, kai Sharif Yahaya Aminu mai shekaru 30 da ke zama a gida mai lamba 26 a kwatas din Sharifai da ke Kano, ka yi wata wallafa don bata wa Musulmi rai a wata kungiyar Whatsapp mai suna Gidan Umma Abiha ta hanyar sakon murya, inda ka kira Annabi da sunan Mushirki, mai yada shirka wanda matsayinsa bai kai na Inyass ba a lahira."

Mai gabatar da kara ya sanar da Daily Trust cewa wanda aka yanke wa hukuncin yana da kwanaki 30 don daukaka kara.

Wani malami mazaunin Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce wannan hukuncin zai tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da daidaito a jihar.

Daurawa, wanda shine tsohon shugaban hukumar Hisbah, ya yi bayanin cewa addini, rayuwar jama'a da dukiya sune wasu sassan da dole a kiyaye don samun zaman lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel