NECO ta fitar da jadawalin jarrabawar ƴan makaranta na shekarar 2020

NECO ta fitar da jadawalin jarrabawar ƴan makaranta na shekarar 2020

Hukumar shirya jarrabawar makarantun sakadandare ta Najeriya, NECO, ta fitar da jadawalin jarrabawar shekarar 2020 da ka'idojin rubuta jarrabawar ta bana.

Hakan na zuwa ne a lokacin da hukumar jarrabawar ta bayyana cewa za ta saka naurar daukan bidiyon sirri na CCTV a dakunan rubuta jarrabawar domin hana magudin jarrabawa.

Rajistara na hukumar, Farfesa Godswill Obioma ne ya sanar da hakan a ranar Talata a Minna yayin gabatar da jadawalin jarrabawar NECO din ta shekarar 2020 kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Obioma ya kuma sanar da ranar rufe yin rajistan jarrabawar inda ya bukaci masu son rubutawa suyi rajista a kan lokaci domin ba za a tsawaita lokacin rajistan ba.

DUBA WANNAN: Yadda wani masanin magunguna ya mutu yayin gasar lalata da karuwa a otel

"Za a fara jarrabawar NECO-BECE ne a ranar Litinin 24 ga watan Agusta a gama a ranar 7 ga watan Satumban 2020.

"Shi kuma jarrabawar fita daga manyan makarantun sakandare, NECO SSCE za a fara ne a ranar 5 ga watan Oktoba a kammala a ranar 18 ga watan Nuwamban 2020.

"Kazalilka, jarrabawar shiga makarantun sakandare, NECE NCEE za a rubuta shi ne a ranar 17 ga watan Oktoban 2020.

"Mun kuma shirya BECE (Ga wadanda za su maimaita) a ranar 11 da 12 ga watan Nuwamban 2020.

"NECO ta kuma shirya tsararren jadawalin dukkan jarrbawar da aka shirya yi ta yadda ba za su ci karo da na jarrabawar WAEC da NABTEB ba.

"Masu ruwa da tsaki da dukkan mutane suna iya sauke jadawalin jarrabawar daga shafin mu ta intanet a www.neco.gov.ng. Mun kuma yi tanadi na musamman ga dalibai makafi da zabiyya.

"Ana janyo hankalin masu ruwa da tsaki da sauran mutane su sani cewa za a rufe yin rajistan BECE kwanaki uku kafin fara jarrabawar. Za a rufe rajistan NCEE mako guda kafin fara jarrabawar yayin da SSCE za a rufe rajistarsa ranar 10 ga watan Satumban 2020 kuma ba za a tswaita ba," in ji Obiano.

Shugaban hukumar jarrabawar ya ce kawo yanzu sun yi wa dalibai 80,110 rajista ta NCEE, 104, 341 kuma BECE yayin da dalibai 169,144 aka yi wa rajistan SSCE.

Ya kuma gargadi daliban suyi dage wurin karatu domin hukumar za ta duba yiwuwar amfani da naurar bidiyon CCTV don kama masu magudin jarrabawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel