Makinde ya sallami Kwamishinan ayyuka da sufuri, Afonja, daga Gwamnatinsa

Makinde ya sallami Kwamishinan ayyuka da sufuri, Afonja, daga Gwamnatinsa

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, ya sallami Mista Raphael Afonja wanda kafin yanzu ya na cikin manyan kwamishinonin da ke tare da shi.

Jaridar The Cable ta ce Injiniya Seyi Makinde ya bada sanarwar tsige kwamishinan ayyuka da sufurin jihar Oyo ne a ranar Litinin, 10 ga watan Agusta, 2020.

Sakataren yada labarai na gwamnan Oyo ya fitar da wannan takardar sallama daga aiki da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin jihar, Olubamiwo Adeosun jiya.

Taiwo Adisa bai bayyana dalilin da ya sa Mai gidansa ya tsige kwamishinan ba. Takardar dai ta ce Afonja zai bar kujerar da ya ke rike da ita ba tare da wata-wata ba.

“Ina so in sanar da kai cewa mai girma gwamna Seyi Makinde ya amince da sallamarka daga kujerar kwamishina, wannan mataki zai fara aiki ba tare da bata lokaci ba.”

Takardar ta kara da: “A dalilin wannan mataki da aka dauka, ana ba ka umarni ka damka duk wasu kayan gwamnati da ke hannunka ga sakataren ma’aikatar sufuri da ayyuka”

KU KARANTA: Idan na mutu a fadi duk abin da aka ga dama game da ni - Obasanjo

Makinde ya sallami Kwamishinan ayyuka da sufuri Afonja daga Gwamnatinsa
Raphael Afonja Hoto: The Cable
Asali: Twitter

“Zan kara da cewa an godewa gudumuwar da ka bada a tsawon lokacin da ka yi a bakin aiki, don haka mu ke yi maka fatan alheri nan gaba."

"Na gode.” Inji gwamnan.

Ba a nan kawai gwamnan ya tsaya ba, ya canzawa wasu kwamishinoninsa biyu ma’aikatu.

Funmilayo Orisadeyi ta bar kujerar kwamishinar kananan hukumomi da masarautu, ta koma kwamishinar ayyukan musamman ayyuka na musamman a gwamnatin Makinde.

A gefe guda kuma, Bayo Lawal ya tashi daga ma’aikatar ayyuka na musamman zuwa ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu da Funmilayo Orisadeyi ta bari.

Idan ba za ku manta ba kwanakin baya aka ji Raphael Afonja ya kamu da COVID-19. Afonja ya shafe kwanaki 55 ya na jinya, dawowarsa ke da wuya aka tsige shi daga ofis.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel