Ajali: Sauran sa'o'i kadan aurensa, ango ya yi mummunan hatsari

Ajali: Sauran sa'o'i kadan aurensa, ango ya yi mummunan hatsari

- Wani ango ya hadu da ajalinsa sakamakon hatsarin mota a karamar hukumar Isoko ta kudu da ke jihar Delta

- Lamari ya afku ne sa'o'i kadan kafin daurin aurensa

- Angon ya tuka motarsa zuwa wani wuri da ke da makwabtaka da yankinsa don fitar da kudi a maimakon ya jira inda ake layi

Wani ango da ke tuki zuwa gida bayan cire kudi, ya rasu a hatsarin mota da ya auku a Oleh, karamar hukumar Isoko ta kudu da ke jihar Delta.

Lamarin ya faru ne sa'o'i kadan kafin daurin aurensa, jaridar The Nation ta ruwaito.

Wata majiya ta ce matashin, wanda ke zama a Ozoro, ya tuka motarsa zuwa wani wuri da ke da makwabtaka da Oleh don fitar da kudi a maimakon ya jira inda ake layi a Ozoro.

Ajali: Sauran sa'o'i kadan aurensa, ango ya yi mummunan hatsari
Ajali: Sauran sa'o'i kadan aurensa, ango ya yi mummunan hatsari Hoto: The Nation
Asali: UGC

A kokarinsa na gaggawar zuwa gida, motar angon ta hantsila a titi inda hakan ya kai ga mutuwarsa.

An gaggauta mika shi asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Wata majiya ta ce mazauna gefen titin ne suka debe kudin da ya watse.

Kakakin 'yan sandan jihar, DSP Onome Onowakpoyeya ya tabbatar da aukuwar lamarin.

KU KARANTA KUMA: Ondo 2020: Bayan kwanaki 48 a PDP, mataimakin gwamna ya sake barin jam'iyyar

A wani labari na daban, mun ji cewa a daren Lahadi, kungiyar 'yan bindiga da suka addabi jihar Katsina sun kai hari a yankin Saulawa da ke karamar hukumar Kurfi ta jihar.

HumAngle ta gano cewa, kungiyar ta mamaye duk wasu wurare na karamar hukumar inda suka fara harbi babu kakkautawa.

A hakan suka kutsa cikin gidaje da shaguna. Majiyoyi da suka zanta da HumAngle sun tabbatar da cewa, kungiyoyin sun sace 'yan mata tare da barin wani mutum da manyan raunika.

Sun yi awon gaba da kayayyakin abinci da wasu abubuwan amfani wanda mallakin 'yan yankin ne.

"An ji harbe-harbe a ko ina a lokacin da nake kiran sallar Isha'i. Hakan yasa dole na daina kiran sallar bayan na ga wasu maza dauke da makamai suna shigowa yankin inda suke wakoki da ihu," mataimakin limamin masallacin Usman Hassan da ke yankin ya sanar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng