Ministan shari’a Malami ya karyata zargin rashawa da ake yi masa

Ministan shari’a Malami ya karyata zargin rashawa da ake yi masa

Antoni janar na tarayya, Abubakar Malami, ya rubuta wasika zuwa ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya bayyana cewa baya cin rashawa ko almubazzaranci da kudade.

Malami, wanda shine ministan shari'a na Najeriya, ya bayyana inda yake samun kudinsa kafin ya zama minista da kuma yadda ya tara dukiyarsa.

Ya yi ikirarin cewa ba ta hanyar rashawa bane ko data daga baitul Mali, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Wasikar ministan ta fito ne a matsayin martani ga wata kungiyar Kanuri, wacce ta yi kira ga Buhari da ya fatattaki AGF a kan zargin rashawa da rashin biyayya da ya zargi dakataccen mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu da shi.

Dakataccen shugaban na EFCC da Malami sun ta kai ruwa rana a kan yaki da rashawa.

Magu ya musanta duk wani zargin da ake masa, amma fadar shugaban kasa ta ce bincikarsa da ake yi na nuna cewa babu saniyar ware a yaki da rashawa na Buhari.

A wasikar Malami, ya yi kira ga shugaban kasar a kan fom na bayyana dukiyarsa da ya bai wa CCB a 2015 a lokacin da aka fara nada shi a matsayin minista.

Ministan shari’a Malami ya karyata zargin rashawa da ake yi masa
Ministan shari’a Malami ya karyata zargin rashawa da ake yi masa Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Ya ce ya rubuta wannan wasikar ne don wanke kansa kuma ya dakile duk wani kokarin bata masa suna da ake yi, wanda yace a halin yanzu ya maka wata wasikar yanar gizo a kotu.

Ya ce, "na yanke shawarar kai korafi gaban kotu sakamakon jerin ababen bacin suna da suka wallafa a kaina. Duk da haka, na rubuta wasika zuwa sifeta janar na 'yan sandan Najeriya don bincike a kan lamarin.

"A hakan, na ji ya zama wajibi na fayyace komai. Saboda irin miyagun maganganu da ke yawo a kaina da yadda na samu dukiyata.

"Akasin hakan mai girma, tun bayan nada ni da aka yi minista, na bayyana dukkan dukiyata biyayya ga wani sashi na kundun tsarin mulki na 1999.

"Daga cikin nasarorina a lokacin da na kwashe shekaru 20 ina aiki, shekaru bakwai a matsayin babban lauyan Najeriya, kafin zama na minista, na shiga kasuwanci.

"Ina da kasuwanci mai kawo kudi na Rayhaan Hotels and Rayhaan Food and Drinks, duk a Kano, tun daga ranar 13 ga watan Disamban 2013. Shekaru da dama kafin shugaba Buhari ya hau mulki har ya nada ni ministansa.

"Tun bayan hawa na minista, na bayyana kadarorina. A matsayina na Antoni janar na tarayya kuma ministan shari'a, na yi alkawarin ci gaba da mutunta ofishina da aikina."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel