Atiku da Frank: Lalube-laluben banza ku ke yi don ku batawa Osinbajo suna – ‘Yan APC
- Wata kungiyar Magoya bayan APC ta zargi ‘Yan adawa da yi wa Yemi Osinbajo sharri
- Kungiyar ta ce Atiku Abubakar da Timi Frank za su bata sunan mataimakin shugaban kasa
Mun samu labari cewa wata kungiya da ke tare da jam’iyyar APC mai mulki, ta zargi Atiku Abubakar da kitsa labarin karya game da mataimakin shugaban kasa
Wannan kungiya ta maida martani ne a kan zargin da ‘yan adawa su ke yadawa na cewa Yemi Osinbajo ya zari kudi har Naira biliyan 10 daga cikin asusun TSA.
Idan za ku tuna a 2015 ne gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fara amfani da asusun bai-daya wanda ake kira TSA domin rage satar dukiyar kasa da ake yi.
Ana zargin tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da fara yada labarin da ke yawo na cewa akwai hannun Osinbajo a bacewar wasu dukiyar gwamnati.
KU KARANTA: Gwamnan da APC ta ke zawarci ya ce ba zai bar PDP ba

Asali: Original
Bayan an fara wannan rade-radi ne tsohon jigon jam’iyyar APC, Timi Frank, ya fito ya na cewa ya kamata mataimakin shugaban kasar ya wanke kan shi daga wannan zargi.
Kungiyar magoya bayan jam’iyyar mai-ci ta maidawa Timi Frank martani, su ka ce darajar da aka san Farfesa Yemi Osinbajo da ita tun ba yau ba, ta isa ta tsaya masa.
A cewar kungiyar, wannan zargi sam ba gaskiya ba ne, sharrin bogi ne kurum wanda babu wata hujja da za ta iya gaskata ta.
Rahoton da aka fitar a yau Litinin ya nuna cewa kungiyar ta bayyana Kwamred Timi Frank a matsayin Karen-farautar tsohon ‘dan takarar shugaban kasa watau Atiku Abubakar.
Ba wannan ba ne karon farko da aka jefi Osinbajo da laifin satar kudin gwamnati. Har yanzu babu wata hujja mai karfi da ta nuna hannun mataimakin shugaban kasar dumu-dumu da laifi.
Masu rajin kare jam’iyyar APC mai mulkin kasar sun ce ‘yan adawar su na harbin iska ne kawai da wannan zargi, kuma hadarinsu ba zai taba zubar da ruwan sama ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng