Jerin 'yan siyasa 4 da Obasanjo ya disashesu a Najeriya

Jerin 'yan siyasa 4 da Obasanjo ya disashesu a Najeriya

Wannan rubutun ra'ayin wani dan jarida mai suna Fredrick Nwabufo ne ba wai na Legit.ng ba. Dan jaridan ya yi sharhi ne a kan karfin ikon cif Olusegun Obasanjo a kasar.

Olusegun Obasanjo babban dan siyasa ne a Najeriya. Yana daya daga cikin 'yan siyasar da suka mori Najeriya kuma ya yi rayuwa cike da tarin damammaki a Najeriya.

Kamar yadda dan jaridar ya fadi ra'ayinsa kuma jaridar The Cable ta wallafa ya ce: "Kaddara ta bai wa Obasanjo turmi da tabarya tare da akalar mulkin Najeriya a 1999, bayan shekaru da dama da aka yi fama da mulkin soji.

"Amma kuma ya yi amfani da damar yadda ya dace? Toh, ya samu damar sauya kasar nan amma kuma yayi hakan cike da ra'ayinsa.

"Mulkin Obasanjo tamkar gyara ne kadan daga mulkin soji. Mulki ne da ke kawar da Duk wani kalubalen da zai iya tasiri a kansa.

"Har a yau, babu wani bayani game da kisan Bola Ige da Harry Marshal tare da wasu kashe-kashe da ake danganawa da fadarsa.

"Sakamakon wannan zubar da jinin ne dattawan arewa suka bukaci Goodluck Jonathan da ya hukunta Obasanjo a 2013.

"Akwai lokutan da dama da Obasanjo ke yanke hukunci bisa ga ra'ayinsa. Lamarin Odi da Zaki Biam inda tsohon shugaban kasar ya tura dakarun soji don mummunan aiki har yau ana maganarsa.

"Babu kunya a lamarin idan Obasanjo yana zargar shugaban kasa Muhammadu Buhari da yanke hukunci da kansa ko kuma yin abu babu duba ga shari'a.

"Rashawa da neman duniya shine tambarin mulkin Obasanjo. Yadda ake siyar da kadarorin gwamnati abun takaici ne. A takaice, halin da wutar lantarki Najeriya ke cike yana da alaka da mulkin Obasanjo.

Jerin 'yan siyasa 4 da Obasanjo ya disashesu a Najeriya
Jerin 'yan siyasa 4 da Obasanjo ya disashesu a Najeriya Hoto: Thisdaylive
Asali: UGC

"Hakazalika, an san Obasanjo da riko da rashin kaunar sasanci. Baya sassautawa makiyi koda kuwa mutuwa yayi. Mummunar wasikar ta'aziyyar da ya aikewa Kashamu abun dogaro ce ga wannna ikirarin.

"A yayin neman fansa, Obasanjo ya yiwa wasu 'yan siyasa murabus na karfi da yaji.

"Ya durkusar da Peter Odili, wanda shine tsohon gwamnan Ribas kuma mai hararo zama mataimakin Umaru Musa Yar'adua. Obasanjo ya saka Jonathan inda ya jefi Odili da zargin rashawa. Dole ta sa Odili ya dakata don tseratar da kansa.

KU KARANTA KUMA: Tuna baya: Obasanjo yana jinjinawa Kashamu tare da fatan alheri (Bidiyo)

"Hakazalika, Obasanjo ya taka rawar gani wurin disashe tauraruwar Atiku Abubakar, mataimakinsa, wanda ya kalubalancesa a kan tazarce. Daga nan ya jefi Atiku da zargin rashawa wanda ya durkusar da siyasarsa har yanzu.

"Akwai Ghali Umar Na'Abba, tsohon kakakin majalisar wakilai da mataimakinsa, Chibudom Nwache, ya disasar da tauraruwarsu bayan sun mika bukatar tsigesa daga kujerar shugaban kasa. Bai sassauta ba sai da ya tabbatar basu koma majalisar ba a 2003.

"Dole a ce Obasanjo ya kware wurin lalata duk wani buri na siyasar abokan hamayya saboda babu shakka kowa na da nasa sirrin."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel