Tuna baya: Obasanjo yana jinjinawa Kashamu tare da fatan alheri (Bidiyo)
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya taba jinjinawa Buruji Kashamu, tsohon Sanata mai wakiltar mazabar Ogun ta gabas, a kan ayyukansa na alheri.
A yayin da ya ziyarci wani shiri na gidauniyar Omo-Illu, wacce mallakin Sanata Kashamu ce, tsohon shugaban kasar ya yi addu'ar fatan alheri ga Kashamu da yake janyo mutane masu tarin yawa zuwa PDP ta halayensa.
An saki bidiyon a 2015 amma babu tabbacin ko yaushe ne aka yi taron.
"Muna godiya da ayyukan da kayi a baya. Ubangiji zai maka sakayya. Ba zai kwashe dukkan abubuwan da kayi ba don karanta mana rai," Obasanjo yace a bidiyon.
Kashamu ya rasu sakamakon fama da yayi da cutar korona a asibitin jihar Legas a ranar Asabar, yana da shekaru 62.
A wata wasika da Obasanjo ya fitar, ya ce rayuwar Kashamu cike take da darussa ga kowa.
Ya zargesa da juya doka da siyasa wurin tserewa shari'a a kan zargin laifukan da ake masa a gida da wajen Najeriya.
A yayin martani ga tsokacin Obasanjo, Ayodele Fayose, tsohon gwamnan jihar Ekiti, ya bukaci Obasanjo da ya daina yi kamar wani waliyyi saboda 'yan Najeriya sun kalmashe hannu suna jiran karshensa.
KU KARANTA KUMA: Sanatoci 3 sun kaurace wa taron jam'iyyar PDP a Ebonyi
Mamacin sun raba hanya da Obasanjo ne a yayin da ake shirin zaben 2015 kuma basu sasanta ba har zuwa rasuwar Kashamu.
A watan Oktoban 2014, Kashamu ya ce mulkin Obasanjo ya bada shaida da ta wankesa a kan zargin ta'ammali da miyagun kwayoyin da ake masa a Ingila.
Ga bidiyon inda Obasanjo yake jinjinawa Kashamu. Yana maganar ne a harshen yarbanci.
A wani labari na daban, sakamakon gwajin cutar korona na tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya fito bayan ya yi martani a kan mutuwar tsohon Kashamu.
Sakamkon ya bayyana dai baya dauke da cutar toshewar numfashin.
A wata takarda da Kehinde Akinyemi, mataimakinsa na musamman a fannin yada labarai ya fitar, ya ce an yi gwajin a ranar Juma'a, 7 ga watan Augustan 2020.
An yi gwajin ne a dakin karatu na Olusegun Obasanjo da ke gidansa na Pent House, Okemosan, Abeokuta, a babban birnin jihar Ogun.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng