Abayomi: Wadanda aka tabbatar sun kamu da COVID-19 sun ki zuwa wurin jinya

Abayomi: Wadanda aka tabbatar sun kamu da COVID-19 sun ki zuwa wurin jinya

- Mutanen Jihar Legas da-dama da su ka kamu da Coronavirus sun ci kafar kare

- Kwamishinan lafiya, Farfesa Akin Abayomi ya bayyana wannan a makon jiya

- Wasu da su ka kamu da cutar sun tsere, kuma watakila su na yadawa Bayin Allah

Kimanin mutanen 1, 455 a Legas da aka tabbatar da cewa su na dauke da kwayar cutar COVID-19 a jikinsu, sun ki zuwa dakunan killace marasa lafiya.

Kwamishinan harkar lafiya na jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi, ya bayyanawa ‘yan jarida wannan labari maras dadi a ranar Asabar, 8 ga watan Agusta, 2020.

A daidai lokacin da shugaban kasa ya tsawaita takunkumin kulle saboda annobar COVID-19, gwamnatin Legas ta na kukan wasu marasa lafiyanta sun tsere.

Kamar yadda Kwamishinan ya yi bayani, bayan an yi wa wadannan mutane 1, 455 gwaji, kuma sakamako ya nuna sun harbu da cutar, sun ki zuwa a kwantar da su a dakunan jinya.

KU KARANTA: Tinubu ya yi magana bayan COVID-19 ta kashe Kashamu

Abayomi: Wadanda aka tabbatar sun kamu da COVID-19 sun ki zuwa wurin jinya
Farfesa Akin Abayomi
Asali: Twitter

Farfesa Akin Abayomi ya ce wadannan marasa lafiya da su ka yi kunnen kashi, su na dauke da cutar a halin yanzu, kuma babu mamaki su na yadawa sauran mutane ciwon.

Da ya ke karin bayani, kwamishinan ya ce yanzu haka akwai mutum 72 da su ka rage cikin masu jinyar COVID-19 da su ke kwance a dakunan da ake lura da marasa lafiya.

Gwamnati ta na da wuraren killace wadanda cutar ta kama su, haka zalika akwai dakunan jinya da ‘yan kasuwa su ka tanada domin yaki da wannnan annoba a jihar Legas.

A makon jiya ne hukumar NCDC ta ce an samu mutane 10, 400 da su ka warke daga COVID-19. Hukumar ta tattara alkaluman ne daga jerin wadanda su ka samu sauki a Legas.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng