Sakamakon gwajin cutar korona na tsohon shugaban kasa Obasanjo ya fito

Sakamakon gwajin cutar korona na tsohon shugaban kasa Obasanjo ya fito

- An yi wa tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo gwajin cutar korona

- Sakamakon gwajin, wanda ya fito a ranar Asabar, 8 ga watan Augusta, ya nuna cewa Obasanjo baya dauke da cutar

- An yi wa tsohon shugaban kasar gwajin ne a dakin karatu na Olusegun Obasanjo

Sakamakon gwajin cutar korona na tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya fito bayan ya yi martani a kan mutuwar tsohon sanata Buruji Kashamu.

Sakamkon ya bayyana dai baya dauke da cutar toshewar numfashin.

A wata takarda da Kehinde Akinyemi, mataimakinsa na musamman a fannin yada labarai ya fitar, ya ce an yi gwajin a ranar Juma'a, 7 ga watan Augustan 2020.

An yi gwajin ne a dakin karatu na Olusegun Obasanjo da ke gidansa na Pent House, Okemosan, Abeokuta, a babban birnin jihar Ogun.

Kamar yadda takardar da Akinyemi ya fitar a ranar Lahadi, 9 ga watan Augusta, ya ce Dr Olukunle Oluwasemowo ne ya dauki samfur din kuma yayi gwajin da ya dawo babu cutar a ranar Asabar.

Sakamakon gwajin cutar korona na tsohon shugaban kasa Obasanjo ya fito
Sakamakon gwajin cutar korona na tsohon shugaban kasa Obasanjo ya fito Hoto: Kehinde Akinyemi
Asali: UGC

"Dakin gwajin na daya daga cikin dakunan gwajin da hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta NCDC ta aminta da su don gwajin cutar korona," takardar tace.

Sakamakon gwajin cutar korona na tsohon shugaban kasa Obasanjo ya fito
Sakamakon gwajin cutar korona na tsohon shugaban kasa Obasanjo ya fito Hoto: Kehinde Akinyemi
Asali: UGC

Legit.ng ta ruwaito cewa, tsohon shugaban kasa Obasanjo a ranar Asabar, 8 ga watan Augusta, ya mika takardar ta'aziiyarsa ga gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, a kan mutuwar Sanata Buruji Kashamu.

Sakamakon gwajin cutar korona na tsohon shugaban kasa Obasanjo ya fito Hoto: Kehinde Akinyemi
Sakamakon gwajin cutar korona na tsohon shugaban kasa Obasanjo ya fito
Asali: UGC

A wasikar mai kwanan wata Asabar, 8 ga Augusta, tsohon shugaban kasar ya bayyana mutuwar Kashamu a matsayin rashin da ba za a iya mayar da shi ba.

Yace: "Rayuwa da tarihin mamacin ya barmu da darrusa da dama."

"Sanata Esho Jinadu (Buruji Kashamu) a rayuwarsa yayi amfani da lauyoyi da siyasa wajen sullubewa doka kan laifukan da aka zargin ya aikata a Najeriya da wajen Najeriya. Amma babu wani wayon lauyoyi, siyasa, al'ada ko ma na likitoci da ya hana mutuwar riskarsa lokacin da mahallici yace lokaci ya yi."

Sai dai kuma da yak martani kan jawabin Obasanjo, Fayose, yace maganar Obasanjo abin kunya ne.

"Abin takaici ne abinda Obasanjo yake fadi kan Buruji Kashamu bayan mutuwarsa don ya san ba zai iya ramawa ba. Me yasa bai fadi hakan lokacin da Kashamu ke raye ba?" Fayose ya ce.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel