Tsaro: Umahi ya soki sauya shugabannin tsaro, ya bai wa Buhari shawara

Tsaro: Umahi ya soki sauya shugabannin tsaro, ya bai wa Buhari shawara

David Umahi, gwamnan jihar Ebonyi, ya soki kiran da ake yi na sauke shugabannin tsaron kasar nan.

A yayin duba ga matsalar tsaron da ke kasar nan, majalisar dattawa ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kori shugabannin tsaro idan suka ki yin murabus.

Amma a yayin jawabi a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi a ranar Juma'a, Umahi ya ce rundunar sojin na bukatar karin kudi ne.

Ya ce shugabannin tsaron sun shirya tsare kasar nan da nagartar ta.

Umahi ya sanar da hakan ne a yayin shagalin bikin bude asibitin sojojin kasa na Najeriya.

Tsaro: Umahi ya soki sauya shugabannin tsaro, ya bai wa Buhari shawara
Tsaro: Umahi ya soki sauya shugabannin tsaro, ya bai wa Buhari shawara Hoto: Vanguard
Asali: UGC

"Ban aminta da abinda majalisar dattawa suke cewa ba na sauya shugabannin tsaro. Abu daya da na sani shine muna bukatar canji a kasar nan sosai. Muna son kowa ya dandana mulki," yace.

"Ba hakan muke bukata ba a wannan lokacin da muke fuskantar kalubalen tsaro. Abinda muke bukata shine tsaron kasa.

"Ba tare da cewa wancan sifeta janar na 'yan sandan Najeriya bai yi aiki ba, gaskiya wannan sifeta janar din na daban ne. Baya tankwaruwa ga dokoki da kuma sharuddan kasar nan. Irin shi ne kasar nan ke bukata. Tabbas shugaban sojan kasa mutum ne mai mayar da hankali."

Umahi ya ce abinda shugabannin tsaro ke bukata a halin yanzu shine bayanai daga jama'a tare da karin kudi don siyan kayan aiki daga gwamnati.

Ya ce korar shugabannin tsaro yanzu zai zama babban kalubale ga yaki da ta'addanci da kuma masu laifuka.

"Toh abinda shugabannin tsaron ke bukata yanzu shine hadin kai da bayanai. Akwai wuya a ce sun dauki mataki ba tare da bayanai ba," yace.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: Mayakan ta'addanci 400 ne suke samun horo a Zamfara da Niger

"Wannan na da amfani kuma a wannan lokacin ko an samu canji, wadanda aka dora ne za su wahala. Ina da tabbacin cewa duk hukuncin da shugabannin tsaron suke dauka ba wai su kadai ke zartar da hukuncin ba.

"A don haka, ina kira ga shugaban kasa da ya goyi bayan ci gaban mulkin shugabannin tsaron tare da kara musu kudi, wanda hakan zai basu karfin guiwa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel