Kotu ta rushe kafatanin shugabannin jam'iyyar APC a jihar Zamfara

Kotu ta rushe kafatanin shugabannin jam'iyyar APC a jihar Zamfara

Wata babbar kotu da ke zamanta a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, ta rushe kafatanin shugabannin jam'iyyar APC na jiha, kananan hukumomi da mazabu.

Kotun ta zartar da wannan hukunci ne a yau, ranar Juma'a, 07 ga watan Agusta, 2020.

Alhaji Surajo da sauran wasu mutane 138 da ke biyayya ga tsohon sanata Kabiru Marafa ne suka shigar da karar shugabancin jam'iyyar APC na jihar Zamfara.

Ma su karar sun yi zargin cewa an tafka magudi tare da hanasu kada kuri'a yayin zaben shugabannin jam'iyyar.

Bayan ya shafe kusan sa'o'i hudu ya na karanta hukuncin da kotu ta yanke, Jastis Bello Tukur Gummi, ya ce Alhaji Surajo da sauran ma su kara sun tabbatarwa da kotu cewa an saba doka tare da hanasu kada kuri'a yayin zaben shugabannin jam'iyya a shekarar 2018.

Kotu ta rushe kafatanin shugabannin jam'iyyar APC a jihar Zamfara
Kotu ta rushe kafatanin shugabannin jam'iyyar APC a jihar Zamfara
Asali: Depositphotos

A saboda hakane kotun ta zartar da hukuncin rushe kafatanin shugabannin jam'iyyar APC da aka zaba a wancan lokacin tare da gargadinsu a kan cigaba da gabatar da kansu a matsayin shugabannin APC na jihar Zamfara.

DUBA WANNAN: 'Yan sandan Bauchi sun azabtar da yarona har ya mutu, suka wurgar da gawarsa'

Kotun ta bayar da umarnin a sake gudanar da sabon zaben shugabannin jam'iyya a matakin jiha, kananan hukumomi da maxabu bisa tsarin gaskiya da girmama doka.

Lauyan ma su kara, Barista Misbahu Salaudeen, ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa kotu ta fahimci cewa an hana mambobin jam'iyya kada kuri'a, wanda hakan ne ya sa ta rushe zaben shugabannin a dukkan matakai.

Sai dai, lauyan shugabannin jam'iyya, Barista Kelechi Odeoyegbo, ya ce zasu nazarci hukuncin kuma zasu iya daukaka kara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel