Gagara: Fusataccen mahaifi ya datse hannun dansa

Gagara: Fusataccen mahaifi ya datse hannun dansa

Wani mutum mai suna Sunday Brown mazaunin yankin Nyomidibi a unguwar Nyangasang da ke garin Calaba, babban birnin jihar Kuros Riba, ya datse hannun dansa mai suna Mathew saboda ya shiga kungiyar tsafi.

Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Alhamis bayan Mista Brown da dansa, Mathew, sun yi fito-na-fito kamar yadda su ka saba.

Wani makwabcin Mista Brown ya shaidawa manema labarai cewa rigimar da ke tsakanin uba da da ta fara zama barazana ga mazauna unguwar, saboda yanzu haka abokan matashin sun fara barazanar daukan fansa.

Majiyar ta bayyana cewa shigar Mathew kungiyar tsafi da sauran halayensa na gagara sune suka jawo mahaifinsa ya datse ma sa hannu.

Gagara: Fusataccen mahaifi ya datse hannun dansa
Gagara: Fusataccen mahaifi ya datse hannun dansa
Asali: Facebook

Wani shugaba a unguwar, Timothy Sam, ya shaidawa manema labarai cewa jami'an rundunar 'yan sanda sun sha kama saboda gagararsa da kuma yawon dare mai cike da alamun tambaya.

"Da sanyin safiyar ranar Alhamis ne Mathew ya kai wa mahaifinsa harin daukan fansa.

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta cafke masu garkuwa da mutane 45 da suka addabi Borno

"Shi kuma mahaifin ya datse masa hannu a kokarinsa na kare kansa," a cewarsa.

Kokarin manema labarai na jin ta bakin mista Brown Mathew bai samu ba.

Kakakin rundunar 'yan sanda, Irene Ugbo, ta ce ba ta samu labarin faruwar lamarin ba, amma ta dauki alkawarin gudanar da bincike.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel