Anambra: Obiano ya sallami Ma’aikatan Hukumar ruwa – Inji Kwamishina

Anambra: Obiano ya sallami Ma’aikatan Hukumar ruwa – Inji Kwamishina

Jaridar Tribine ta rahoto cewa sama da ma’aikata 1000 da ke aiki da tsohuwar hukumar ruwa na jihar Anambra aka sallama daga aiki.

Gwamnatin Anambra ta raba wadannan ma’aikata da hanyar samun abincinsu ne da sunan rashin gaskiya wajen mu’amala da dukiyar hukumar ruwan.

Kwamishinan harkar ruwa na Anambra, Mista Emeka Ezenwanne, ya shaida wannan lokacin da ya gabatar da takardar sallamar a gaban ‘yan jarida a makon nan.

A ranar Alhamis, Emeka Ezenwanne ya tabbatarwa manema labarai cewa an kori wadannan ma’aikata ne domin sun gaza bayanin inda kudin ruwa su ka shige.

Kwamishinan ya zargi ma’aikatan da aka sallama da batar da kudin da hukumar ruwan ta ke da shi, ya ce ba su sauke alhakin mutanen jihar da ke kansu ba.

“Hukumar ruwa ta zama abin da ta zama, ba ta aiki ne saboda facakar shugabannin ta.” inji Emeka Ezenwanne.

KU KARANTA: Bincike: Hukumar NDDC ta yi bindiga da Naira Biliyan 2 cikin kwanaki 100

Anambra: Obiano ya sallami Ma’aikatan Hukumar ruwa – Inji Kwamishina
Jihar Anambra
Asali: UGC

“Haka kuma ba su iya yin bayanin inda kudin da su ka karba daga hannun gwamnati ya shige ba.” Kwamishinan ya ce EFCC ta na binciken lamarin yanzu haka.

Ezenwanne ya kara da cewa: “An sallame su ne saboda ainihin yadda su ke aiki, wanda hakan ya shafi dokar ruwa da gwamnatin jihar Anambra ta kawo a 2015.”

Duk da an sallami ma’aikata masu dinbin yawa, kwamishinan ya ce gwamnati ta na cigaba da kai ruwan fanfo ga kauyuka 179 karkashin wasu hukumomi na jihar.

Ezenwanne ya ja-kunnen sauran ma’aikatu su ba gwamnatin mai girma gwamna Willie Obiano goyon bayan a yunkurin da ya ke yi na inganta rayuwar al’umma.

Da aka yi magana da wani tsohon ma’aikacin hukumar, ya ce sun koma su na aiki da gwamnatin jiha, kuma su na bin bashin albashinsu tun daga 2012 har yau.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel