Rahoto: Akwai wala-wala a game da ainihin abin da Hukumar Neja-Delta ta batar
Bayanan da su ke fitowa daga babban bankin Najeriya na kasa watau CBN da ofishin babban akawun gwamnatin tarayya sun kara haska badakalar NDDC.
CBN da OAGF sun nuna cewa shugabannin rikon kwarya na hukumar NDDC sun batar da Naira biliyan 2.1 da sunan yada labarai daga Oktoban 2019 zuwa Mayun 2020.
Rahoton da jaridar Punch ta fitar ya nuna cewa hukumar NDDC a takardun da ta gabatar gaban kwamitin binciken majalisar dattawa ta ce ta kashe Naira Biliyan 1.1 ne.
Daga cikin wannan makudan kudi da aka batar wajen yada labaran, NDDC ta kashe Naira miliyan 17 ne a karkashin shugabancin Joi Nunieh a cikin watanni biyar.
Hukumar ta batar da ragowar kudin na Naira biliyan biyu ne daga ranar 19 ga watan Fubrairunn 19 zuwa 31 ga watan Mayu, duk an yi wannan ne a shekarar nan.
Rahoton da aka fitar ya na cewa: “A lura cewa kudin da aka batar ya kai kusan Naira biliyan 2.1 kamar yadda takardun CBN da OAGF su ka nuna.”
KUU KARANTA: Barnar da na gani a NDDC ta sa na ajiye aiki na - Kwankwaso
”Wannan ya nuna cewa hukumar NDDC ta boyewa gwamnati gaskiyar abin da ta kashe.”
Abin da hukumar ta fada shi ne: “NDDC a karkashin shugabannin rikon kwaryan farko, ta kashe N17m wajen yada labarai, yayin da sababbin shugabannin su ka kashe N1.1bn.”
An samu sabani tsakanin CBN da OAGF da ita kanta hukumar ta NDDC game da gaskiyar gaba daya kudin da aka kashe a tsawon wa’adin shugabannin rikon kwarya.
Misali, CBN ta gabatar da takardun da ke nuna an kashe N92, 233,216,061, OAGF ya ce N82, 495, 259, 314 aka kashe, yayin da NDDC su ke ikirarin sun batar da N81, 549, 894, 866 ne.
Kwanaki majalisar wakilai ta fara binciken zargin badakalar da aka tafka a hukumar, a wurin wannan bincike ne Farfesa Kemebradikumo Daniel Pondei ya suma.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng