Kotu ta ci tarar Azeez Fashola da Awouga saboda sabawa dokar COVID-19

Kotu ta ci tarar Azeez Fashola da Awouga saboda sabawa dokar COVID-19

A ranar Alhamis, 7 ga watan Agusta, 2020, dakarun ‘yan sanda na jihar Legas su ka gurfanar da Azeez Fashola wanda aka fi sani da Naira Marley a kotu.

An gurfanar da shararren Mawakin ne tare da Manajansa, Seyi Awouga, bisa zargin rashin bin dokar kullen da gwamnati ta sa domin yaki da annobar COVID-19

Kamar yadda kakakin ‘yan sandan jihar Legas, ya bayyana, ana zargin mutanen biyu ne da laifin yi wa matakan da aka sa na yaki da annobar COVID-19 kunnen kashi.

Bala ElKana ya fitar da jawabi a madadin rundunar ‘yan sanda, ya ce an gurfanar da Naira Marley da Seyi Awouga a gaban kotun laifuffukan musamman da ke Oshodi.

Wadanda ake zargin sun taka harabar kotun da aka kafa domin sauraran irin wadannan laifuffukan ne da kimanin karfe 3:30 na rana inji ElKana.

A ranar 13 ga watan Yuni, wannan Mawaki ya taka kafarsa daga Legas zuwa Abuja, ya kuma dawo garin Legas a wannan rana ta filin jirgin sama na Murtala Muhammad.

Kotu ta ci tarar Azeez Fashola da Awouga saboda sabawa dokar COVID-19
Azeez Fashola wanda aka fi sani da Naira Marley
Asali: Instagram

KU KARANTA: Ana neman Naira Marley a kotu da zargin hannu a laifin sata

Tafiyar da Tauraron yayi a tsakiyar lokacin da ake fama da Coronavirus a Najeriya, ba ta da wani muhimmanci. Asali ma ya halarci wani biki ne da aka shirya a birnin tarayyar.

Ba yau ne Tauraron ya fara samun kansa a matsala da hukuma ba. Naira Marley ya na cikin wadanda su ka halarci haramtaccen bikin da Funke Akindele ta shirya kwanaki.

A dalilin wannan jami’an tsaro su ka kai Fashola kotu tare da Abokin aikin na sa, domin su amsa laifin da ke kansu na bijirewa umarnin shugaban kasa na zaman kulle.

Laifin ya ci karo da sashe na 4(i) na dokokin jihar Legas na yaki da miyagun cututtuka. Duk wanda aka samu da laifi, za a iya hukunta shi a karkashin sashe na 58 na dokar lafiya a jihar.

A karshe dukkaninsu biyu sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa, don haka Alkali ya ci su tarar kudi N100, 000.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel