Boko Haram: Mayakan ta'addanci 400 ne suke samun horo a Zamfara da Niger

Boko Haram: Mayakan ta'addanci 400 ne suke samun horo a Zamfara da Niger

Bayan rahotannin da jaridar HumAngle ta fitar wanda take bayyana abubuwan da ke faruwa a kungiyar Jama'atu Ahlil Sunnah Lidda'awati Wal Jihad, ko kuma sashen Boko Haram na Shekau, wani sabon abun mamaki ya biyo baya.

A yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya, an gano cewa akwai mayakan Boko Haram 400 a jihohin Zamfara da Neja a watan Yulin 2020.

Yawan mayakan ta'addancin a yankin bai hada da Ansaru ba balle Al-Qaeda da aka ce suna da kungiyoyi masu alaka a yankin arewa maso yamma da arewa tsa tsakiya tun da dadewa ba, HumAngle ta ruwaito.

Har a halin yanzu, ba a san yawan mayakan ISWAP da sauran kungiyoyin jihadin da ke yankin wadanda suke amfani da wannan lokacin wurin shigowa da makamai da sauran kayayyakin bukatarsu.

Kamar yadda binciken ya nuna, mayakan Boko Haram 400 da ke samun horon sun hada da manyan kwamandoji, na tsakiya da kuma daruruwan sojoji.

HumAngle ta gano cewa, mayakan Boko Haram da ke jihohin Neja da Zamfara basu riga sun samu makamai ba har zuwa karshen watan Yuli, amma suna ci gaba da horar da mayaka kuma za su mallaki makaman, wata majiya ta tabbatar.

Hakazalika, kungiyar na ci gaba da samun mambobi a yankin arewa maso yamma da kuma jihohin da ke da makwabtaka da jamhuriyar Nijar don kara karfinta.

Sassan kungiyar da ke jihohin Neja da Zamfara na kokarin ganin sun aiwatar da hare-hare kamar yadda ake yi a yankunan arewa maso gabas, binciken ya nuna.

Boko Haram: Mayakan ta'addanci 400 ne suke samun horo a Zamfara da Niger
Boko Haram: Mayakan ta'addanci 400 ne suke samun horo a Zamfara da Niger. Hoto daga HumAngle
Asali: UGC

KU KARANTA: Boko Haram: 'Yan sanda sun damke Mallum, mai samarwa 'yan ta'adda kayan bukata

Legit.ng ta ruwaito cewa, rahotanni na yawo cewa wasu dinbin ‘tan ta’addan kungiyar Boko Haram na bangaren Abubakar Shekau, sun fitar da sabon bidiyo na musamman.

‘Yan ta’addan da su ka yi wa Abubakar Shekau mubaya'a sun ce sun dauki wannan bidiyo ne a jihar Neja da ke a yankin Arewa maso tsakiyar kasar.

Malam Audu Bulama Bukarti, wani masanin harkar tsaro ya bayyana wannan a shafinsa na Twitter dazu.

A wannan bidiyo an ga mutane kimanin dari su na gabatar da sallar idi a kungurmin daji. Daga baya wasu sojoji uku su ka yi jawabin barka da sallah. Wadannan mayaka sun yi magana ne da harshen Hausa, Ingilishi da kuma Fulfulde.

Bukarti wanda yanzu haka ya ke tare da cibiyar Tony Blair da ke Landan, ya ce idan har ta tabbata ‘Yan ta’addan sun ratsa jihar Neja, Najeriya ta na fuskantar barazana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel