Kotu za ta saurari karar da ke neman a kori shari’ar El-Zakzaky a ranar Juma’a

Kotu za ta saurari karar da ke neman a kori shari’ar El-Zakzaky a ranar Juma’a

- Babbar kotu da ke Kaduna za ta saurari kara a kan bukatar da aka mika gabanta na korar shari'ar shugaban Shi'a, Sheikh Ibraheem Zakzaky

- An nemi a kori shari'ar wanda gwamnatin tarayya ta mika saboda rashin bada shaida kwakwara

- Kotun za ta saurari karar ne a ranar Juma'a, 6 ga watan Agusta

Wata babbar kotu da ke Kaduna za ta saurari shari'a a kan wata bukata da aka mika gabanta na korar shari'ar Sheikh Ibraheem Zakzaky, shugaban mabiya akidar Shi'a wanda gwamnatin tarayya ta mika saboda rashin bada shaida kwakwara.

Sheikh Zakzaky da matarsa Zeenat, suna tsare tun a 2015 bayan arangamar da mabiyansa suka yi da dakarun sojin kasa a Zaria, jihar Kaduna.

Femi Falana (SAN), ya bukaci kotun da tayi watsi da wadannan zargin da ake wa Zakzaky bisa dogaro da sashi na 36 na kundin tsarin mulkin kasar nan.

Kotu za ta saurari karar da ke neman a kori shari’ar El-Zakzaky a ranar Juma’a
Kotu za ta saurari karar da ke neman a kori shari’ar El-Zakzaky a ranar Juma’a Hoto: Tehran Times
Asali: UGC

Ya kamata kotun ta saurari shari'a a ranar Alhamis da ta gabata amma sai ta fada ranar hutun shagalin babbar sallah.

Bukatar farko da lauyan Zakzaky ya mika ita ce, "a yi watsi da karar saboda kasa bayyana laifi takamaimai da masu kara suka yi wanda hakan ya ci karo da sashe na 36, sakin layi na 8 da na 12 na kundun tsarin mulkin kasar nan.

"Bukata ga kotun wurin watsi da zargin na biyu baki dayansa saboda kasa mika shaida da tayi a kan laifin ko alakanta mai kare kansa da shaidun da suka bayyana."

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: INEC ta bude shafin yanar gizo da za a iya kallon sakamakon zabe kai tsaye

Falana na bukatar kotun da ta yi watsi da dukkan zargin da ake wa wanda yake karewa.

Lauyan na bukatar kotun da ta saki wanda yake karewa saboda rashin lafiya da yake fama da ita.

A wani labari na daban, hedkwatar hukumar yan sandan Najeriya ta saki jawabin cewa yan kungiyar Shi'ar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ta IMN kadai suka hana gudanar da muzahara ba sauran kungiyoyin Shi'a ba.

Sifeto Janar na hukumar ya bayyana hakan ne ta baki mai magana da yawun hukumar, Frank Mba, a jawabin da ya saki da ranar Talata, 10 ga watan Satumba 2019.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel