Jarumta: 'Yan kauye sun yi wa 'yan bindiga mugun duka, sun kashe daya a Katsina

Jarumta: 'Yan kauye sun yi wa 'yan bindiga mugun duka, sun kashe daya a Katsina

Wani mutum wanda ake zargin dan bindigar daji ne ya hadu da ajalinsa sakamakon rikicin da ya barke tsakanin kungiyarsa da 'yan sa kai a kauyen Garwa a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Mazaunan kauyen sun ce wata kungiyar 'yan bindigar sun tsinkayi kauyen a daren Litinin, inda suka kashe shugaban matasa na APC na gundumar Yau-Yau/Mallamawa, Mallam Sidi.

An gano cewa wasu kauyawan tare da 'yan sa kai sun yi fito na fito da 'yan bindigar.

Wani mazaunin kauyen ya ce, "Yan sa kan sun kashe dan bindiga daya yayin arangama inda sauran suka tsere cikin daji ba tare da daukar komai ba."

Kakakin Rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da wannan ci gaban, duk da bai bada karin bayani game da hakan ba.

"Tabbas, hakan ta faru," ya bada tabbaci da aka tambayesa.

Amma kuma, har yanzu 'yan sanda basu yi martani a kan wani rahoto da ke fitowa ba da ke bayyana cewa 'yan bindiga sun kutsa kauyukan Sanawa Vera da Dogon Ruwa a karamar hukumar Dutsin-Ma ba ta jihar a safiyar Alhamis.

Jarumta: 'Yan kuaye sun sun yi wa 'yan bindiga lilis, sun kashe daya a Katsina
Jarumta: 'Yan kuaye sun sun yi wa 'yan bindiga lilis, sun kashe daya a Katsina. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

KU KARANTA: Fani-Kayode: Sarkin Shinkafi ya amince da murabus din masu sarauta 5, ya maye gurbinsu

Kakakin Rundunar 'yan sandan ya ce, a bashi lokaci don ya gano gaskiyar lamarin daga ofishin 'yan sandan yankin.

Ya ce, "Ku bani lokaci in binciki yadda al'amarin ya faru daga ofishin 'yan sandan yankin."

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Borno ta kama wasu 'yan ta'adda 45 a sassa daban-daban na jihar a kan laifuka daban-daban da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane.

Daya daga cikin 'yan ta'addan mai suna Goni Mallum, ya amsa laifinsa na samarwa 'yan ta'addan kayayyakin bukatu amma ya ce yunwa da fatara ce ta sa shi yin hakan.

Mallum ya ce 'yan ta'addan sun kama shi a kan hanyarsa ta zuwa gona amma sun yanke shawarar kyale shi idan ya amince zai dinga yi musu aike-aike a kyauta, lamarin da ya kasa musantawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel