Sarkin Kano da Sarkin Bichi sun kai ziyarar mubaya'a ga sarkin Gwandu

Sarkin Kano da Sarkin Bichi sun kai ziyarar mubaya'a ga sarkin Gwandu

Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, da takwaransa na Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, sun kai ziyarar mubaya'a ga sarkin Gwandu, mai martaba Muhammad Iliyasu Bashar.

Sarakunan biyu 'yan uwan juna sun kai ziyarar ne a yau, Alhamis, 6 ga watan Agusta, 2020, kamar yadda wata sanarwa daga majiyar fadar ta wallafa a shafin sada zumunta (tuwita).

Alhaji Muhamad Bashar, tsohon soja a rundunar soji ta Najeriya, ya zama sarkin Gwamdu a shekarar 2005 bayan tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya tsige tsohon sarki, Mustapha Jokolo Haruna.

Mai martaba Bashar ne sarkin Gwamndu na 20 tun bayan kafuwar masarautar a karni na 18.

A cikin watan Yuli ne Legit.ng ta wallafa rahoton cewa naɗe-naɗen da mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya yi sun jawo abin magana.

Wani masanin tarihi ya ce masarautar Kano ta tsumbula cikin harkar siyasa.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya nada Aminu Babba dan Agundi a matsayin Sarkin Dawaki Babba wanda ya na cikin manyan 'yan majalisar sarkin Kano. Wannan nadi ya bar baya da kura.

A shekarar 2003 ne Marigayi Ado Bayero watau mahaifin Sarki mai-ci, ya tunbukewa Babba dan Agundi rawaninsa na Sarkin Dawaki mai tuta kuma Hakimi a kasar Gabasawa.

Sarkin Kano da Sarkin Bichi sun kai ziyarar mubaya'a ga sarkin Gwandu
Sarkin Kano da Sarkin Bichi
Asali: Twitter

A wancan lokacin, Ado Bayero ya zargi Aminu Babba dan Agundi da rashin biyayya da shiga cikin siyasa.

Tsohon Sarkin Dawakin ya shafe shekaru ya na shari’a da masarautar Kano.

DUBA WANNAN: Fusatattun matasa sun farke rufin majalisar Edo, sun sace sandar iko

Bayan hawan Muhammadu Sanusi II kan mulki ne ya daukaka kara zuwa kotun koli inda Alkali ya tabbatar da hukuncin da marigayi Ado Bayero ya yanke, kuma masarauta ta amince da hakan.

Abin mamaki sai aka ji cewa Alhaji Aminu Ado Bayero zai yi wa Aminu Babba dan Agundi naɗin Sarkin Dawaki Babba wanda ake ke ganin an ci mutuncin fada.

Dr. Tijjani Mohammad Naniya, Masani a jami’ar Bayero ta Kano, ya yi hira da BBC Hausa, inda ya bayyana cewa ba a taba maidawa mutum rawani bayan an cire shi daga sarauta ba.

A cewar Tijjani Mohammad Naniya, wannan mataki da sabon sarkin Kano ya dauka abin kunya ne, kuma tamkar yi wa mahaifinsa watau Sarki Ado Bayero tsirara ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel