Mazauna Katsina sun sake gudanar da zanga-zanga kan hauhawan rashin tsaro
Fusatattun matasa a safiyar yau Alhamis, 6 ga watan Agusta sun toshe babban hanyar Kankara-Katsina, inda suka gudanar da zanga-zanga a kan hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa garuruwansu.
Mutanen sun yi amfani da manyan reshen bishiyoyi wajen kewaye hanyar kauyen Marken Dogon Ruwa a karamar hukumar Dutsima, inda suka dunga komar da masu motoci daga bangarori biyu na hanyar.
A yanzu haka daruruwan masu motoci da masu tafiya suna nan sun yi cirko-cirko a hanyar.
‘Yan fashi sun kai mamaya kauyukan Sanawa, Bera, Turare da Dogon Ruwa da ke karamar hukumar Dutsinma a daren ranar Laraba.

Asali: UGC
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wata tawagar ‘yan sanda daga rundunar tsaron ta isa wajen, inda take kokarin tausar mutanen domin a bude hanyar.
Wannan shine karo na biyar da mazauna Katsina ke zanga-zanga kan rashin tsaro a jihar cikin watanni biyu da suka gabata.
An gudanar da zanga-zanga a garin Daddara da ke karamar hukumar Jibia, Yantumaki da ke karamar hukumar Danmusa da kuma Yankara da ke karamar hukumar Faskari.
KU KARANTA KUMA: Kada ku raba kan ahlinmu – Iyalan Obaseki sun karyata goyon bayan Ize-Iyamu
A baya mun ji cewa Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja a ranar Laraba.
Masari ya ce ba za a bari kallubalen tsaro da ake fama da ita a jihohin Arewa maso Yamma da Arewa maso tsakiya ya tabarbare kamar matsayin da Boko Haram ya kai a Arewa maso Gabas.
Masari ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke amsa tambayar manema labarai a gidan gwamnatin bayan kammala taro da Shugaba Muhammadu Buhari a Abuja.
Ya ce a halin yanzu ana daukan dukkan matakan da suka dace domin kawo karshen hare haren yan bindiga da wasu laifukan a yankin na Arewa maso Yammacin kasar.
Gwamnan ya ce za a samu amfanin gona mai kyau a bana duk da cewa yan bindiga da wasu bata gari sun adabi manoma a kimanin kananan hukumomi tara a jihar ta Katsina.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng