‘Yan sanda sun mamaye majalisar dokokin Edo ne saboda shaharar Obaseki - PDP
- Jam’iyyar PDP ta yi martani a kan dalilin da ya sa jami’an ‘yan sanda suka mamaye majalisar dokokin jihar Edo a ranar Alhamis, 6 ga watan Agusta
- Babbar jam’iyyar adawar ta bayyana cewa wannan aikin jam’iyyar APC ne
- Ta bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki na martani ne ga shaharar Gwamna Godwin Obaseki
Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Edo ta yi martani a kan mamaye majalisar dokokin jihar da ‘yan sanda suka yi a ranar Alhamis, 6 ga watan Agusta.
Babbar jam’iyyar adawar, a shafinta na Twitter, ta yi ikirarin cewa mamaye majalisar da aka yi ya kasance aikin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne.
A cewar PDP, hakan na faruwa ne sakamakon shaharar da Gwamna Godwin Obaseki ke samu.
KU KARANTA KUMA: Ya zama dole shugabanni su dunga daukar gyara - Sultan na Sokoto
Ta wallafa a shafin nata cewa: “Labari da dumi-dumi! Sakamakon shaharar da @GovernorObaseki na jihar Edo ya yi da kuma tarin karbuwar da yake samu daga mutanensa, gwamnatin tarayya da jam’iyyar @OfficialAPCNg ke jagoranta sun tura ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro domin su mamaye majalisar dokokin jihar. Wannan ba abun yarda bane."
KU KARANTA KUMA: Kada ku raba kan ahlinmu – Iyalan Obaseki sun karyata goyon bayan Ize-Iyamu
Da farko dai mun kawo maku cewa 'Yan sanda sun mamaye farfajiyar majalisar jihar Edo, sa'o'i kadan bayan tsige mataimakin kakakin majalisar, Yekini Idiaye.
Yan majalisar jihar sun tsige Idiaye ne a ranar Laraba yayin zaman majalisar a Benin City.
Dan majalisar mai wakiltar mazabar Akoko-Edo ta 1 da wasu 'yan majalisa hudu a ranar Litinin sun bayyana goyon bayansu ga Fasto Osagie Ize-Iyamu.
Wadanda suka bi ayarin Idiaye sune Emmanuel Agbaje mai wakiltar mazabar Akoko-Edo ta biyu, Nosayaba Okunbor mai wakiltar mazabar Orhionmwon ta gabas.
Sai kuma Dumez Ugiagbe mai wakiltar mazabar Ovia ta arewa maso gabas. Duk sun bayanna goyon bayansu ga Fasto Ize-Iyamu a gidan sa da ke Benin.
Amma kuma Roland Asoro, mai wakiltar mazabar Orhionmwon II an nada shi a matsayin mataimakin kakakin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng