Ya zama dole shugabanni su dunga daukar gyara - Sultan na Sokoto

Ya zama dole shugabanni su dunga daukar gyara - Sultan na Sokoto

- Sultan Sokoto Muhammadu Sa'ad Abubakar ya shawarci shugabanni da su dinga sauraron shawara

- Sa'ad Abubakar ya jadadda cewa jagoranci na bukatar gyara a koda yaushe

- Ya yi kira ga jama'ar Kano da su rungumi shugabanninsu na gargajiya a matsayin zabin Allah kuma su yi musu addu'a nagari

Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa'ad Abubakar ya shawarci shugabanni da su dinga sauraron shawara, ganin cewa shugabanci yana bukatar gyara a koda yaushe.

Ya bada wannan shawarar ne yayin karbar bakuncin sarakunan Kano da Bichi wadanda suka kai masa ziyara don jaddada goyon bayansu garesa.

Basaraken ya yi kira ga shugabanni da su saka tsoron Allah a duk abinda suke yi saboda akwai ranar kin dillanci, ranar da za su tsaya a gaban Allah su yi bayani a kan yadda suka shugabanci al'umma.

Sarkin Musulmi ya bayar da muhimmiyar shawara ga shugabanni
Sarkin Musulmi ya bayar da muhimmiyar shawara ga shugabanni Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya yi kira ga jama'ar Kano da su rungumi shugabanninsu na gargajiya a matsayin zabin Allah kuma su yi musu addu'a nagari.

"Wannan sauyin ya yuwu ne da izinin Allah. Ina so ku rungumi hakan da imani tare da fatan nasara ga shugabannin," yace.

KU KARANTA KUMA: Kwamitin Salami ya yi alkawarin sauraron Magu, ya yi watsi da wata bukatar da ya mika

Sarkin Musulmin ya yi kira ga 'yan majalisar sarakunan da su dinga basu shawara nagari, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

"Ba za mu ce mun cika dari bisa dari ba. Muna yin kuskure don haka muna bukatar shawara. Za mu gyara idan mun san mun yi kuskure.

"Ya kamata jama'armu su yi hakuri sannan su dinga tausayinmu tare da mana addu'ar Allah ya kare mu tare da yi mana jagora. Wannan ne ya dace kowanne Musulmi nagari ya yi wa shugabansa," sarkin Musulmin ya jaddada.

Sarkin Musulmi Sa'ad ya tuna da alakar da ke tsakanin masarautar Kano da Sokoto wacce ta wuce shekaru 200 da suka gabata.

A wani labarin kuma, Shugabannin addinin Musulunci da na Kirista sun nuna rashin jin dadinsu game da yadda ake rasa rayuka da dinbin dukiyoyin Bayin Allah a Najeriya.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto a ranar Talata cewa shugabannin sun gargadi gwamnatin tarayya a game da yadda makamai su ke barkowa cikin kasar nan.

Shugaban kungiyar CAN ta Kiristoci, Rabaren Samson Ayokunle da Muhammadu Sa’ad Abubakar III sun yi magana game da lamarin a ranar 4 ga watan Agusta, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel