Kwamitin Salami ya yi alkawarin sauraron Magu, ya yi watsi da wata bukatar da ya mika

Kwamitin Salami ya yi alkawarin sauraron Magu, ya yi watsi da wata bukatar da ya mika

- Kwamitin fadar shugaban kasa da ke binciken Ibrahim Magu, dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa, ya ce zai tabbatar da ganin ya saurare shi

- Sai dai kwamitin ya ki amsa bukatar Magu na neman a nadi zaman da za su yi a faifan bidiyo

- A cewar kwamitin bai san manufar Magu na neman a nadi zaman ba

- An dai kama Magu tare da tsaresa a ranar Litinin, 6 ga watan Yulin 2020, bayan kiran gaggawa da kwamitin fadar shugaban kasar ta yi masa

Kwamitin bincike na fadar shugaban kasa a kan Ibrahim Magu, dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa, ya ce zai tabbatar da ganin ya saurare shi (Magu)

Kwamitin, wanda ya samu shugabancin Ayo Salami, tsohon shugaban kotun daukaka kara, su ke bincikar Magu.

A yayin zaman, Wata majiya daga kwamitin ta sanar da TheCable cewa kwamitin ya ki amincewa da nadar al'amarin a bidiyo, amma an tabbatar masa da cewa za a sauraresa.

"Mambobin kwamitin ba gurfanar da Magu suka yi ba ko EFCC," majiyar ta sanar daga bakin Salami.

"Ba wurin gurfanarwa bane, kwamiti ne da ke da alhakin bincike. Bukatar Magu na cewa a nadi zaman a bidiyo. Hakan ba zai yuwu ba saboda kwamitin bai san amfanin nadar ba.

Kwamitin Salami ya yi alkawarin sauraron Magu, ya yi watsi da wata bukatar da ya mika
Kwamitin Salami ya yi alkawarin sauraron Magu, ya yi watsi da wata bukatar da ya mika Hoto: The Cable
Asali: UGC

"Wurin zaman ba na dindindin bane kuma ba zai yuwu a saka kayayyakin nadar zaman ba kamar yadda Magu ya bukata. Ko a manyan kotu ba a saka irin wadannan kayayyakin.

"Kwamitin ya dauki alwashin sauraron Magu da dukkan abubuwan da zai sanar."

An kama Magu tare da tsaresa a ranar Litinin, 6 ga watan Yulin 2020, bayan kiran gaggawa da kwamitin fadar shugaban kasar ta yi masa.

Antoni janar na tarayya kuma ministan shari'a ya mika korafi gaban shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan wasu jerin zargi da ake ma Magu.

KU KARANTA KUMA: Za mu karbo N96bn da aka sace a mulkin Ajimobi - Makinde

Ana zarginsa da handamewa tare da killace wasu kadarori da aka samo daga wurin mahandaman kasar nan.

Ana zarginsa da siyan wata kadara a Dubai amma ya musanta dukkan zargin da ake masa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng