Za mu karbo N96bn da aka sace a mulkin Ajimobi - Makinde

Za mu karbo N96bn da aka sace a mulkin Ajimobi - Makinde

Seyi Makinde, gwamnan jihar Oyo, ya ce zai tabbatar da ganin cewar an dawo da makuden biloyoyin naira na jihar da yake zargin an sace karkashin mulkin marigayi Abiola Ajimobi.

Ajimobi ya rasu a watan Yuni bayan kamuwa da ya yi da cutar sarkewar numfashi ta korona.

A yayin jawabi a taron kaddamar da ginin babbar hanyar Ajia zuwa Airport da ke Ife a garin Ajia, gwamnan ya ce za a yi amfani da kudin idan an samosu wajen inganta ababen more rayuwa na jihar.

Jaridar The Cable ta tattaro cewa Gwamna Makinde ya yi jawabi a kan caccakarsa da ake yi a kan N100 biliyan da aka bai wa jihar.

"Mulkin mu da gaske yake. Za mu yi kokari wurin inganta ababen more rayuwa a jihar Oyo a cikin kankanin lokaci. Ta hakan ne masu zuba hannayen jari za su fuskanto mu," Taiwo Adisa, sakataren yada labarai na gwamnan ya sanar a madadinsa.

Za mu karbo N96bn da aka sace a mulkin Ajimobi - Makinde
Za mu karbo N96bn da aka sace a mulkin Ajimobi - Makinde Hoto: PM Parrot
Asali: UGC

"Don cimma wannan burin, dole ne mu sake tsara yadda zamu kashewa ababen more rayuwar jihar kudi saboda abinda muke karba daga Abuja a kowanne wata ba ya isarmu mu biya albashin ma'aikatar.

"Don haka sabon tsarin yadda zamu inganta rayuwar mu a jihar shine abinda ya dace.

"Na ji wasu suna kalubalantar mu a rediyo a kan N100 biliyan da muka karba kuma suna zargin muna son saka su a bashi ne. Ina tunanin yakamata su sani cewa Makinde ba haka yake ba.

"A shekaru takwas da suka yi suna mulki, sun mayar da hankali ne a kan yadda za su kwashe naira biliyan daya a kowanne wata zuwa aljihunsu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sojoji da ‘yan sanda sun kama masu zanga-zanga a Abuja

"Sun kwashe watanni 96 a ofis, hakan na nufin N96 biliyan ta jihar Oyo na tare da su. Za mu karbo kudinmu don habbaka ababen more rayuwa.

"Don haka mu sanar da hukumar yaki da rashawa ta jihar Oyo na nan biye da su. Ina so in tabbatar muku da cewa kudaden jihar da aka handame za su dawo kuma zamu amfana."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel