Yanzu Yanzu: Sojoji da ‘yan sanda sun kama masu zanga-zanga a Abuja

Yanzu Yanzu: Sojoji da ‘yan sanda sun kama masu zanga-zanga a Abuja

- Sojoji da 'yan sanda sun kama masu zanga-zangar juyin juya hali wato 'RevolutionNow' a birnin Abuja

- Mambobin kungiyar dai na gudanar da zanga-zanga ne a yau Laraba, 5 ga watan Agusta a wasu jihohin kasar

- A kano kuma, mun ji cewa an tsananta tsaro a wasu sassa saboda shirin zanga-zangar juyin juya hali da ake yi a babban birnin jihar

Jami'an tsaro da suka hada da sojoji da 'yan sanda sun damke masu zanga-zangar lumana na juyin juya hali wato 'RevolutionNow' a birnin Abuja a ranar Laraba, 5 ga watan Agusta.

Masu zanga-zangar wadanda suka fito rike da takardu masu dauke da rubuce-rubuce tun wurin karfe 8:00 na safe sun bukaci shugabanci nagari.

Wasu daga cikin takardun an rubuta, "Yan Najeriya na fama da cuta da talauci, rashin adalci da kuma mace-mace. Bamu amince da rashin adalci ba. Matasa na rayuwa babu aikin yi."

Da yawa daga cikin masu zanga-zangar sun sanya hula launin ruwan goro sannan suka hadu a Unity Fountain da ke kan titin Shehu Shagari a Maitama.

Yanzu Yanzu: Sojoji da ‘yan sanda sun kama masu zanga-zanga a Abuja
Yanzu Yanzu: Sojoji da ‘yan sanda sun kama masu zanga-zanga a Abuja Hoto: Sahara Reporters
Asali: UGC

Za su fara zanga-zangar kenan 'yan sandan suka isa wurin tare da tarwatsa su, jaridar Punch ta ruwaito.

Sojoji da sauran jami'an tsaro sun mamaye titunan da suka hada da na Aguiyi Ironsi don hana masu zanga-zangar yawo.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo: Buhari ya gayyaci Ize-Iyamu yayinda ake shirin fara kamfen

Lauya mai rajin kare hakkin dan Adam, Tope Akinyode, ya ce ya ga lokacin da jami'an tsaro ke dukan masu zanga-zangar babu dalili.

Akinyode ya ce, "an kama a kalla mutum 29 daga cikin mutanen. Jami'an tsaro sun kwantar da su kasa inda suka dinga dukansu. Ko a matsayina na lauya sun ci zarafina."

An gano cewa ana gudanar da irin wannan zanga-zangar a sauran jihohin kasar nan har da Legas.

A shekarar da ta gabata ne aka kama Omoyele Sowore, shugaban juyin juya hali na RevolutionNow inda ya kwashe watanni uku a tsare.

A kano kuma, mun ji cewa an tsananta tsaro a wasu sassa saboda shirin zanga-zangar juyin juya hali da ake yi a babban birnin jihar.

Ýan sanda dauke da makamai da kuma jami'an NSCDC sun mamaye Fadar Lado da shataletalen Dangi da ke kan titin Zaria tare da wasu sassan jihar tun karfe 6:30 na safe.

A wata wallafa da Omoyele Sowore, shugaban kungiyar yayi a shafinsa na Twitter a ranar Talata, ya bayyana Fadar Lado da ke kan titin Zaria a matsayin wurin haduwa na jihar Kano.

Kakakin NSCDC na jihar Kano, ASC Ibrahim Idris Abdullahi ya tabbatar da cewa aikin hadin guiwar an fara sa ne sakamakon bayanan sirrin da aka samu a kan kungiyar.

A lokacin rubuta wannan rahoton, babu alamar zanga-zangar a babban birnin jihar don kowa na ci gaba da ayyukansa. Amma kuma jami'an tsaro sun tsananta tsaro a fadin jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel