El-Rufa'i ya mayarwa da sarakunan kudancin Kaduna martani a kan zargin kwace kasa

El-Rufa'i ya mayarwa da sarakunan kudancin Kaduna martani a kan zargin kwace kasa

Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya kalubalanci ma su rike da sarautar gargajiya a kudancin jihar a kan su nuna wani wuri da aka kwace a yankunansu tare da mikawa wasu mutane ko kungiyoyi ba bisa ka'ida ba.

Kazalika, El-Rufa'i ya kalubalanci sarakunan su bawa hukumomi da jami'an tsaro goyon baya a kokarinsu na tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kudancin jihar Kaduna.

Ya zaburar dasu a kan su zama ma su adalci ga duk jama'ar da ke zaune a karkashin masarautunsu.

El-Rufa'i ya yi wadannan furuci ne a matsayin martani a kan zargin cewa wasu mutane sun kwace wasu sassan kudancin jihar Kaduna mai fama da yawaitar hare - hare a 'yan kwanakin baya bayan nan.

El-Rufa'i ya mayarwa da sarakunan kudancin Kaduna martani a kan zargin kwace kasa
El-Rufa'i
Asali: Depositphotos

Gwamnan ya fadi hakan ne ranar Talata yayin ganawarsa da majalisar sarakunan jihar, inda ya bayyana cewa gwamnatinsa ta dauki duk mazaunin wani yanki a matsayin dan jiha kamar yadda kundin mulki ya amince.

DUBA WANNAN: Magance matsalar tsaro: Buhari ya bada umurnin yin garambawul a rundunonin tsaro

Ya jaddada cewa yada labaran karya a kan gaskiyar halin da kudancin Kaduna ke ciki ba zai kashe gwuiwar gwamnatinsa a kokarinta na kawo karshen rikicin da aka shafe kusan shekara 40 ana fama da shi.

El-Rufa'i ya bayyana bakin cikinsa a kan yadda ake yada labarin karya a kan kwace gonaki da filayen jama'ar kudancn Kaduna.

Ya ce an fara amfani da wannan labarin karya a lokacin da rikici ya taba barkewa a yankin a shekarar 2016/2017.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel