Wasu 'ya'yan jam'iyyar PDP a Edo sun bukaci ICPC ta binciki Obaseki
Wasu mambobin jam'iyyar PDP karkashin inuwar wata kungiyar masu ruwa da tsaki ta jihar Edo, ta mika korafi ga hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta.
'Ya'yan jam'iyyar sun nemi hukumar da ta binciki Gwamna Godwin Obaseki a kan zarginsa da ake da waskar da wasu makuden kudade.
Sun bukaci a binciki gwamnan a kan wata kwangilar da ya bai wa kamfaninsa mai suna Afrilnvest Ltd.
Amma mai bada shawara ga Obaseki a fannin yada labarai, Crusoe Osagie, ya ce wannan korafin sharri ne wanda jam'iyyar APC ke shiryawa don bata sunan gwamnan.
Ya ce kokarin janye hankalin ubangidansa ba zai yi tasiri ba.
Andrew Egboigbe, wani mamba a jam'iyyar PDP a gunduma ta uku ta karamar hukumar Orhionmwon, ne ya mika korafin ga ICPC a ranar Litinin.
Korafin mai bayyana yadda Obaseki ya mika kwangila ga kamfaninsa, ya zarge shi da amfani da karfin kujerarsa ba ta yadda ya dace ba wajen bai wa kansa kwangilar.
A korafin, an zargi Obaseki da zama mamallakin kamfanin Afrinvest kuma cewa yana amfani da hakan wurin bai wa kansa kwangila tare da kara kudin ta ba tare da bin ka'idar kundin tsarin mulki ba wurin bada kwangilar.
KU KARANTA KUMA: A binciki sarakunan gargajiya a yankunan da rashin tsaro ya tsananta - Sanata Gobir
"A matsayinmu na 'yan jihar Edo masu kishi, bamu da inda za mu kira gida da ya wuce jihar Edo. Muna mika korafin nan a kan gwamnan jiharmu da kamfaninsa na Afrinvest Ltd.
"Wannan ya biyo bayan ganowa da muka yi cewa gwamnan na amfani da kujerarsa wurin bai wa kamfaninsa kwangiloli da ayyukan ci gaban amma yana waddaka da kudin ba ta yadda ya dace ba," yace.
A wani labarin, Gwamna Godwin Obaseki, ya ja kunnen 'yan siyasa da ke shirin tada zaune tsaye a jihar da su sauya tunani ko kuma su riski tashin hankali.
A wata tattaunawa da aka yi da Obaseki, wanda shine dan takarar zaben gwamna a jihar Edo karkashin jam'iyyar PDP, ya jaddada cewa a shirye yake ya damke duk wanda zai tada hankali a jihar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng