Wike: Ba za mu biyewa batun yanki da tsarin kama-kama a zaben Shugaban kasa ba

Wike: Ba za mu biyewa batun yanki da tsarin kama-kama a zaben Shugaban kasa ba

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya ce babban abin da ke gaban babbar jam’iyyar hamayya ta PDP shi ne tsara yadda za ta lashe zaben shugaban kasa a 2023.

Nyesom Wike ya ce jam’iyyar PDP za ta nemi hanyar da za ta bi ta yi nasara a zabe mai zuwa na 2023 ba wai ta tsaya ta na la’akari da yankin da ‘dan takararta zai fito ba.

Wike wanda shi ne shugaban kwamitin yakin neman zaben PDP a jihar Edo, ya yi wannan bayani ne lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Channels TV jiya.

Da ya ke jawabi a ranar Talata, gwamnan na jihar Ribas ya ce jam’iyyar da ta ke kan mulki ce kurum za ta ta iya tsaida yankin da zai fito da ‘dan takarar shugaban kasa.

An tado gardamar zaben 2023 ne bayan Mamman Daura ya fito ya na kira ga APC ta yi watsi da tsarin kama-kama, ta fito da duk wanda ya fi cancanta ya yi takara a 2023.

KU KARANTA: 2023: Atiku zai sake takarar Shugaban kasa a zabe mai zuwa

Wike: Ba za mu biyewa batun yanki da tsarin kama-kama a zaben Shugaban kasa ba
Nyesom Wike Hoto: Twitter
Asali: Facebook

Wike cewa ya yi: “A matsayinmu na jam’iyyar adawa, za mu duba duk abubuwan da ke kasa; abubuwan da za su taimaka mu lashe zabe ne tukuna."

"Wannan shi ne muhimmin abu a gare mu. Jam’iyyar da ke kan mulki za su iya cewa haka (za ayi kama-kama), amma ga masu adawa, akwai abubuwan dubawa.”

Ko da jam’iyyar PDP ta warewa ‘Yan Arewa tikitin takarar shugaban kasa a zaben 2019, Wike ya na ganin cewa ba dole ba ne a 2023, tsarin kama-kama ya yi aiki.

Gwamnan ya ke cewa: "Abubuwa da yawa za su yi tasiri. Saboda haka kuskure ne a matsayina na ‘dan adawa in ce dole sai an yi wannan yanzu, ba zan ce haka ba.”

Jaridar Daily Trust ta ce mataimakin sakataren yada labarai na PDP, Diran Odeyemi, ya shaida mata cewa jam’iyyarsu za ta yi duba da yankin da za a ba takara.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng