A binciki sarakunan gargajiya a yankunan da rashin tsaro ya tsananta - Sanata Gobir
- Shugaban kwamitin majalisa dattawa na tsaron kasa, Ibrahim Abdullahi Gobir ya nemi gwamnati da ta binciki sarakunan gargajiya a yankunan da rashin tsaro ya tsananta
- Gobir ya yi zargin cewa akwai laifin wasu daga cikin sarakunan gargajiya a hare-haren da ake kaiwa
- Ya kuma jadadda cewa baya goyon bayan sasanci kowanne iri da 'yan bindiga
Shugaban kwamitin majalisa dattawa na tsaron kasa, Ibrahim Abdullahi Gobir, ya yi kira ga bincike na musamman don tabbatar da rawar da wasu sarakunan gargajiya ke takawa wurin assasa lalacewar tsaro a yankunan su.
A yayin jawabi a kan yadda 'yan bindigar daji suka addabi yankinsa na Sokoto ta gabas, Gobir ya ce akwai laifin wasu daga cikin sarakunan gargajiya a hare-haren da ake kaiwa.
"A gaskiya wasu daga cikin sarakunan gargajiya na yankin na da hannu kuma ababen zargi ne. Ina bada shawarar a bincikesu sosai musamman a yankunan da 'yan bindiga suka addabi al'umma.
"Gwamnati ta bincikesu tare da gano rawar da suka taka sannan ta bayyana miyagu a cikinsu saboda ba zai yuwu mu daura dukkan laifi akan gwamnati ba," yace.
KU KARANTA KUMA: Abinda yasa Atiku, Saraki da Kwankwaso ba za su koma APC ba
Ya kara da cewa, "gwamnati na yin abinda ya dace amma akwai zagon kasa a al'amarin. Don haka dole ne mu gano su waye a boye."
Gobir wanda ke amsa tambayoyin manema labarai a gidan sa da ke Sokoto ya ce baya goyon bayan sasanci kowanne iri da 'yan bindiga.
Kamar yadda yace, "za a iya sasanci da mai kare hakkin jama'arsa saboda yana son rayuwarsu ta inganta ne. Amma wadannan mutanen kisa suke babu dalili."
Gobir ya ce bai taba tsammanin irin wannan kisan a arewa ba musamman a jihar Sokoto.
Ya nuna damuwarsa matuka a kan kashe-kashen wanda a cewarsa zai iya kawo yunwa nan gaba saboda manoma na tsoron zuwa gonakinsu.
A bangaren batun sallamar shugabannin tsaro kuwa, ya ce suna nan a kan bakansu. "Muna son zaman lafiya ga kowa ta yadda za ka iya tafiya har zuwa Abuja ba tare da jami'an tsaro ba kuma ka kai lafiya."
Ya jinjinawa dakarun sojin Najeriya a kan nasarorin da suke samu wurin yaki da 'yan bindiga.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng