Tauraron Juventus Cristiano Ronaldo ya yi tunanin komawa taka leda a PSG

Tauraron Juventus Cristiano Ronaldo ya yi tunanin komawa taka leda a PSG

- ‘Dan wasa Cristiano Ronaldo ya yi gigin barin Juventus kwanakin baya

- Ronaldo ya yi tunanin komawa kungiyar PSG sai kuma abin bai yiwu ba

- Annobar COVID-19 ce ta hana a karkare cinikin saida babban ‘dan wasan

Sababbin rahotanni su na zuwa cewa kwanaki Cristiano Ronaldo ya kai ga tunanin tashi daga kungiyar Juventus kusan shekaru biyu kacal da zuwansa kulob din.

Ana rade-radin ‘dan wasan gaban na kasar Portugal ya so ya koma PSG inda zai hadu da shararrun taurarin Duniya irinsu Neymar Jr. da kuma Kylian Mbappe

A karshe wannan buri na ‘dan kwallon mai shekara 35 bai cika ba, a sakamakon annobar COVID-19 da ta barke a Duniya, ta kuma jagula lamarin kasuwanci.

Bayan abubuwa sun lafa, an cigaba da buga wasanni amma Ronaldo bai samu damar barin kungiyar ta sa ba, har ta kai 'dan wasan ya ci gasar Seria A a karshen kaka.

KU KARANTA: Napoli za ta kashe kudi wajen sayen 'Dan wasan Najeriya

Tauraron Juventus Cristiano Ronaldo ya yi tunanin komawa taka leda a PSG
Cristiano Ronaldo da Seria A Hoto: Juventus
Asali: Facebook

Alamu sun nuna Ronaldo ba ya jin dadin yadda abubuwa su ka rika tafiya a birnin Turin, don haka ne ya soma lissafin yadda zai bar Italiya ya koma Faransa.

A karshe Ronaldo ya nuna bajinta a kakar bana, inda ya zuba kwallaye 31 a gasar cin kofin Italiya. Ciro Immobile ne kurum ya sha gaban ‘dan wasan a yawan kwallaye.

Tun ya na bugawa Real Madrid, Tauraron ya na da sha’awar buga kwallo tare da Neymar wanda kungiyar ta rika zawarci tun ya na tare da kungiyar Santos a Brazil.

Shi kuma Kylian Mbappe bai taba boye sha’awarsa ta kaunar Ronaldo ba. ‘Dan wasan gaban ya na cikin matasa masu tasowa da ake ji da su yanzu a Duniyar kwallo.

Bugu da kari, Ronaldo ya na kaunar birnin Faransa musamman ganin cewa a nan ne ya yi nasarar lashe gasar kofin Turai na Euro shekaru hudu da su ka wuce.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel