Zaben Edo: Idan rikici suke so za mu nuna masu rikici - Obaseki

Zaben Edo: Idan rikici suke so za mu nuna masu rikici - Obaseki

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ja kunnen 'yan siyasa da ke shirin tada zaune tsaye a jihar da su sauya tunani ko kuma su riski tashin hankali.

A wata tattaunawa da aka yi da Obaseki, wanda shine dan takarar zaben gwamna a jihar Edo karkashin jam'iyyar PDP, ya jaddada cewa a shirye yake ya damke duk wanda zai tada hankali a jihar.

Kamar yadda jaridar Punch ta wallafa, Gwamnan ya ce, "babu wanda ya isa ya tada tarzoma. Idan suna son tarzoma, a shirye muke da mu basu.

"Duk wanda ka ga ya tarwatsa mota saboda fosta ta tana kai, a sanar da ni. Tabbas zan nuna masa cewa mune a gwamnatin."

Obaseki ya kara da cewa shi da mataimakinsa, Philip Shuaibu a shirye suke kuma su kadai ne gatan jihar.

Zaben Edo: Idan rikici suke so za mu nuna masu rikici - Obaseki
Zaben Edo: Idan rikici suke so za mu nuna masu rikici - Obaseki Hoto: Premium Times
Asali: UGC

"Ni ne gwamna kuma Philip ne mataimakina. Mu kadai ne a jihar nan muke da kariya kuma muna jan kunnen ga duk wanda ke son yin abinda bai dace ba. Za mu kama shi sannan a ladabtar da shi."

Amma kuma, ya zargi jam'iyyar APC da kin yin kamfen amma kuma sun kare da yada farfaganda, karya da tashin hankali saboda suna hango faduwa a zaben 2020 da za a yi.

KU KARANTA KUMA: Abinda yasa Atiku, Saraki da Kwankwaso ba za su koma APC ba

Idan za ku tuna a baya mun kawo maku cewa Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, ya bayyana cewa babu wani mutum da yake jin tsoro sai Allah.

Da yake magana yayinda ya karbi bakuncin shugabannin addinin Musulunci a gidan gwamnati da ke Benin, a ranar Juma’a, gwamnan ya zargi Shugaban jam’iyyar APC a jihar da shigo da makamai domin tsorata magoya bayansa.

Ya ce a shirye yake da ya tsaya da mutanensa da kuma kare ra’ayinsu.

Obaseki zai kara da Osagie Ize-Iyamu, abokin adawarsa na APC, a zaben ranar 19 ga watan Satumba.

Har ila yau wasu daga cikin yan uwan Gwamna Obaseki biyu sun marawa Ize-Iyamu baya a zaben da za a yi na jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel