'Ba 'yan Boko Haram ne su ka kai min hari ba' - Gwamna Zulum ya fasa kwai

'Ba 'yan Boko Haram ne su ka kai min hari ba' - Gwamna Zulum ya fasa kwai

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya dora alhakin harin da aka kaiwa tawagarsa ranar Laraba ta makon jiya a kan sojojin Najeriya.

A ranar Larabar makon jiya ne aka kaiwa tawagar gwamna Zulum hari yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa garin Baga da ke karkashin karamar hukumar Kukawa a jihar Borno.

Jaridar Premium Times ta rawaito cewa Zulum ya tsallake rijiya da baya yayin da aka kaiwa tawagarsa hari yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa Baga domin rabon tallafi ga mazauna sansanin gudun hijira (IDP).

Da ya ke magana da kwamandan rundunar soji jim kadan bayan kaiwa tawagarsa harin, Gwamna Zulum ya nuna bacin ransa a kan yadda sojoji su ka gaza kwace garin Baga duk fa yawan rundunoninsu da ke jibge a yankin.

'Ba 'yan Boko Haram ne su ka kai min hari ba' - Gwamna Zulum ya fasa kwai
Gwamna Zulum
Asali: Facebook

"Kun fi shekara guda a nan wurin, akwai sojoji 1,181 a wannan yankin, idan ba za ku iya kwace garin Baga mai nisan kilomita 5 daga sansaninku ba, sai mu hakura mu manta da Baga.

"Zan sanar da bbban hafsan rundunar soji idan ya so sai ya sauyawa sojojin da ke nan wurin da za a amfanesu," kamar yadda gidan Talabijin na Channels ya rawaito Zulum na fadawa kwamandan sojojin.

DUBA WANNAN: El-Rufa'i ya mayarwa da sarakunan kudancin Kaduna martani a kan zargin kwace kasa

Da ya ke magana kwana daya bayan kai ma sa harin, Zulum ya ce abinda ya faru a kansa ba wani abu ba ne face kitimurmurar sojoji.

Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne yayin da wasu gwamnonin jam'iyyar APC a karkashin jagorancin shugabansu, Atiku Bagudu gwamnan jihar Kebbi, su ka kai ma sa ziyarar jaje a fadar gwamnatin jihar Borno da ke Maiduguri.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel