COVID-19: Kungiya mai zaman kanta ta ce NCDC ta kashe miliyan 39.75 wajen siyan motar SUV

COVID-19: Kungiya mai zaman kanta ta ce NCDC ta kashe miliyan 39.75 wajen siyan motar SUV

- Wata kungiya mai zaman kanta mai suna BudgIT ta nuna damuwa kan kashe-kashen kudi da hukumar NDCD ke yi a baya-bayan nan

- BudgIT, ta daya daga cikin dandamalinta CivicHive, ta ce hukumar NCDC ta siya wani babban motar Jeep a kan farashin naira miliyan 39.75

- Kungiyar ta kuma nuna damuwa game da kashe-kashen da wasu hukumomin gwamnati ke yi a yan kwanakin bayan nan wanda ya kai naira biliyan 3.03

Wata kungiya mai zaman kanta mai suna BudgIT ta nuna damuwa kan siyan mota kirar Prado jeep da cibiyar kula da hana yaduwar cututtuka (NCDC) ta yi.

BudgIT wacce kan bibiyi kashe kudaden gwamnati ta daya daga cikin shafukanta, CivicHive ta dasa ayar tambaya kan dalilin da yasa hukumar NCDC a Abuja ta siya motar Prado jeep da ya kai naira miliyan 39.75.

Kungiyar mai zaman kanta ta nemi sanin dalilin da yasa hukumar lafiyar ta kashe wannan kudin wajen siyan abun hawa.

COVID-19: Kungiya mai zaman kanta ta ce NCDC ta kashe miliyan 39.75 wajen siyan motar SUV
COVID-19: Kungiya mai zaman kanta ta ce NCDC ta kashe miliyan 39.75 wajen siyan motar SUV Hoto: NCDC
Asali: Twitter

“Menene amfanin motar Prado Jeep a tsakiyar annoba? Akwai bukatar @NCDCgov ta yi wa jama’a bayanin amfaninsa,” kungiyar ta nemi ba’asi.

Ta kuma nuna damuka kan kashe-kashe da hukumomin ma’aikatu da hukumomin gwamnati ke yi wanda yawansu ya kai naira biliyan 3.03 kan kwangilolin COVID-19.

KU KARANTA KUMA: Badakalar NDDC: Akpabio ya saki sabbin sunaye, ya ambaci tsoffin gwamnoni 3 da suka samu kwangiloli

A halin da ake ciki, Chikwe Ihekweazu, darakta janar na hukumar NCDC ya bayyana cewa gaskiya batu game da cutar korona a kasar shine cewa cutar za ta shafe akalla shekara daya.

Ihekweazu ya bayyana hakan ne a lokacin zantawa da kwamitin Shugaban kasa kan Covid-19 a Abuja a ranar Juma’a, 24 ga watan Yuli, jaridar The Nation ta ruwaito.

Shugaban na NCDC ya bayyana cewa zai fi kyau ga asibitoci a kasar su zauna da gaskiyar lamari maimakon korar marasa lafiya dake tsananin bukatar kulawar likitoci.

Zuwa yanzu dai jimillar masu cutar ta kai 43,841 a fadin kasar nan. Mutum 20,308 ne suka warke garas daga jinyar cutar yayin da mutum 808 suka riga mu gidan gaskiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel