Bikin sallah: Sanata Shehu Sani ya wallafa hotunan kyawawan ‘ya’yansa

Bikin sallah: Sanata Shehu Sani ya wallafa hotunan kyawawan ‘ya’yansa

- A kwanan nan ne Sanata Shehu Sani ya wallafa hotunan kyawawan ‘ya’yansa

- Dan siyasan na Najeriya kuma mawallafi, ya bi sahun miliyoyin Musulmai wajen yin bikin Sallah babba

- Sani ya wallafa hotunan ne a shafinsa na Instagram

A yan kwanakin da suka gabata ne daukacin al’umman Musulmi a fadin duniya suka yi bikin Sallah babba kuma ba a bar Najeriya ba a baya wajen yin ado da kwaliyya.

Daya daga cikin irin wadannan mutane da basu bari an barsu a baya ba wajen bikin shine sanatan Najeriya, Shehu Sani.

Ya kayatar da zukata da dama a yanar gizo bayan ya je shafinsa na Instagram, inda ya wallafa hotunan kyawawan yaransa; maza biyu da mata biyu.

KU KARANTA KUMA: Babu wani mutum da nake tsaro sai Allah – Gwamna Obaseki

Bikin sallah: Sanata Shehu Sani ya wallafa hotunan kyawawan ‘ya’yansa
Bikin sallah: Sanata Shehu Sani ya wallafa hotunan kyawawan ‘ya’yansa Hoto: Shehu Sani
Asali: Instagram

A hotunan, mazan sun fito cikin shiga ta babbar riga da huluna kalar launin ruwan kasa yayinda matan suka sanya leshi ruwan madara da launin ruwan kasa da kuma kallabi.

Sani wanda ya kasance marubuci kuma mai kare hakkin dan Adam, shine Shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam na Najeriya kuma Shugaban kungiyar Hand-in-Hand, Africa.

Ya kasance kan gaba wajen fafutukar dawo da damokradiyya a Najeriya.

Duk da annobar da ake ciki, an yi bikin babbar sallah da tarin kwalam da makulashe tsakanin ‘yan uwa da abokan arziki.

KU KARANTA KUMA: 'Yan Najeriya basu fahimci ra'ayin Mamman Daura ba kan tsarin shugabanci - Tsohon Gwamna

A wani labarin kuma, mun kawo maku cewa ma’abota shafukan sadarwar zamani sun shiga santi na kyawun ‘ya’yan Bashir El-Rufai, daya daga cikin ‘yan uwan gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai.

Shahararren mai daukar hoton nan, George Okoro ne ya dauki kyawawan matan hotunan.

A cikin hotunan, an gano ‘yan uwan junan su shida cikin shiga iri guda na wandon Jean da riga mai launin ruwan kasa.

‘Yan uwan junan sun yi kama da mawakan turai a hotunan harma mai hoton na tambayar sunan da ya dace a kira su da shi.

An saki hotunan ne a lokacin bikin babbar sallah.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel