Babu wani mutum da nake tsaro sai Allah – Gwamna Obaseki

Babu wani mutum da nake tsaro sai Allah – Gwamna Obaseki

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, ya bayyana cewa babu wani mutum da yake jin tsoro sai Allah.

Da yake magana yayinda ya karbi bakuncin shugabannin addinin Musulunci a gidan gwamnati da ke Benin, a ranar Juma’a, gwamnan ya zargi Shugaban jam’iyyar APC a jihar da shigo da makamai domin tsorata magoya bayansa.

Ya ce a shirye yake da ya tsaya da mutanensa da kuma kare ra’ayinsu.

“Bana tsoron kowani mutum sai Allah. Na san hadewar don a tunzurani da magoyana bayana ne amma ba za mu fada a tarkonsu ba domin Allah zai taimake mu,” in ji shi.

“A yanzu haka da nake maku magana, za ku yi mamakin cewa tuni yan sanda daga Abuja suka zo jihar, kuma an biya su domin su kama magoya bayanmu. Wani biloniya ne ya biya su domin su kama magoya bayan jam’iyyar Peoples Democratic Party a jihar.

“Wannan biloniya shine ya dauki nauyin hare-haren da aka kaimun tare da gwamnonin PDP a fada. Hakan zai fada maku matakin da rashawa ya kai.

Babu wani mutum da nake tsaro sai Allah – Gwamna Obaseki
Babu wani mutum da nake tsaro sai Allah – Gwamna Obaseki Hoto: Premium Times
Asali: UGC

“Suna shirin haddasa rikici, kawo makamai, da kuma tsoratar da magoya bayanmu duk a cikin tsarinsu. Sun san cewa idan aka yi zabe na gaskiya da amana, ba za su kai labari ba. Dabararsu shine ci gaba da farfaganda da karairayinsu.

“Sun san cewa basu da wani abun nunawa; shirinsu shine tsoratar da magoya bayanmu da tabbatar da ganin cewa basu je wajen jefa kuri’u ba.

“Sun kai wa magoya bayana hari sannan suka so su mayar da martani ga harin. Ba zan kai masu hari ba a matsayina na Shugaban tsaro na jihar, hakkina ne wanzar da zaman lafiya. Za mu ci gaba da hakan a kowani hali.”

Obaseki zai kara da Osagie Ize-Iyamu, abokin adawarsa na APC, a zaben ranar 19 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: 'Yan Najeriya basu fahimci ra'ayin Mamman Daura ba kan tsarin shugabanci - Tsohon Gwamna

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamna Godwin Obaseki ya rasa goyon bayan wasu ‘yan uwansa biyu gabannin zaben gwamnan jihar Edo.

Mazajen biyu masu suna Osaro Obaseki da Victor Obaseki sun kasance makusantan gwamnan na jihar Edo.

Sun zabi goyon bayan babban abokin adawar gwamnan, Fasto Osagie Ize-Iyamu, wanda yake dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), PM News ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng