An tura karin ‘yan sanda zuwa kananan hukumomi 5 a Kaduna saboda kashe-kashe
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, Umar Muri, ya tura karin ‘yan sanda zuwa yankin kudancin jihar a yayinda ake fama da kashe-kashe a yankin.
Yankunan sun hada da kananan hukumomi biyar na Kajuru, Zango-Kataf, Kaura, Kauru, da Jemaa.
Kwamishinan ya ce tura jami’an na daga cikin kokari da ake na dawo da doka a yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula a jihar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Hakan ya biyo bayan umurnin Sufeto Janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu, wanda ya umurci kwamishinan ‘yan sandan Kaduna da ya tura karin jami’ai a kan wadanda ke kasa.

Asali: UGC
Baya ga Kajuru, kananan hukumomi hudu da suka hada da Zango-Kataf, Kaura, Kauru da Jemaa, na fuskantar hare-hare a ‘yan kwanakin nan, wanda hakan ya tursasa gwamnatin jihar sanya dokar kulle na sa’o’i 24 a garuruwan.
KU KARANTA KUMA: Zafafan hotunan ‘ya’yan dan uwan Gwamna Nasir El-Rufai su 6
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammed Jalige, a wata sanarwa da ya saki a ranar Juma’a, ya ce: “Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, Umar Muri ya yi umurnin tura karin jami’ai cikin gaggawa zuwa kananan hukumomin Kajuru, Zango Kataf, Kaura da Kauru da ke jihar daga cikin kokarin dawo da doka a yankunan da abun ya shafa, sakamakon hare-haren kwanan nan da sauran matsalolin tsaro.
“Kwamishinan ‘yan sanda ya umurci dukkanin kwamandoji da shugabannin yan sanda a yankunan da abun ya shafa, da su yi amfani da jami’an da aka tura yadda ya kamata wajen kare rayuka da dukiyoyi, da kuma tabbatar da bin dokar kulle na sa’o’i 24 da gwamnatin Kaduna ta sanya.
“Kwamishinan ‘yan sandan na yi wa mutanen jihar Kaduna, musamman wadanda suka rasa masoyansu da dukiyarsu sakamakon wannan rikicin jaje.
"Ya kuma ci gaba da basu tabbacin cewa rundunar za ta yi duk abunda za ta iya don tabbatar da warzuwar zaman lafiya a yankunan da abun ya shafa.
“Hakazalika, kwamishinan na umurtan mutanen jihar masu bin doka da su ba ‘yan sanda, sojoji da sauran hukumomin tsaro hadin kai, yayinda suke gudanar da ayyukansu na tabbatar da doka domin karesu.
“Ya kuma gargadi fitinannu a jihar da su guji ayyukan da ka iya haddasa rikici da take doka, yayinda yace rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda ya addabi mutanen jihar da fitina.”
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng