Zafafan hotunan ‘ya’yan dan uwan Gwamna Nasir El-Rufai su 6

Zafafan hotunan ‘ya’yan dan uwan Gwamna Nasir El-Rufai su 6

- Shakka babu matan arewa na da kyawu na musamman da babu mai iya karbewa daga garesu

- Wannan ne dalilin da yasa hotunan kyawawan ‘ya’yan dan uwan gwamnan jihar Kaduna su shida ya karade shafukan zumunta

- Kyawawan ‘yan matan su shida sun je gidan daukar hoto suka dauki zafafan hotunan wanda aka saki lokacin bikin babban sallah

Ma’abota shafukan sadarwar zamani sun shiga santi na kyawun ‘ya’yan Bashir El-Rufai, daya daga cikin ‘yan uwan gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai.

Shahararren mai daukar hoton nan, George Okoro ne ya dauki kyawawan matan hotunan.

A cikin hotunan, an gano ‘yan uwan junan su shida cikin shiga iri guda na wandon Jean da riga mai launin ruwan kasa.

Zafafan hotunan ‘ya’yan dan uwan Gwamna Nasir El-Rufai su 6
Zafafan hotunan ‘ya’yan dan uwan Gwamna Nasir El-Rufai su 6 Hoto: George Okoro
Asali: Instagram

‘Yan uwan junan sun yi kama da mawakan turai a hotunan harma mai hoton na tambayar sunan da ya dace a kira su da shi.

KU KARANTA KUMA: Sanata Ndume ya goyi bayan samun shugaban kasa daga kudu a 2023

An saki hotunan ne a lokacin bikin babbar sallah.

A wani labari na daban, mun ji cewa shugaba Muhammadu Buhari ya yi sallar Idi Eid El-Kabir tare da iyalansa da wasu hadimansa a gidan gwamnati da ke birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA KUMA: Masu fyade 27 sun shiga hannun ‘yan sanda a jihar Bauchi

Shugaban kasar ya ce ya yi hakan ne domin bin shawarwarin kwamitinsa ta yaki da Covid 19, PTF, da kuma kwamitin koli da harkokin addinin musulunci (NSCIA).

Shugaban kasar ya yi amfani da shafinsa na Twitter a ranar Juma'a, ya taya alumma murnar bikin sallar:

"Na yi Sallar Idi a gida tare da iyalai na a safiyar yau bisa shawarwarin kwamitin shugaban kasa ta yaki da Covid 19, PTF, da kuma kwamitin koli da harkokin addinin musulunci (NSCIA). Ina taya mu murnar Sallar baki daya."

Limamin masallacin gidan gwamnati, Abdulwaheed Suleiman ne ya jagorancin sallar ta rakaa biyu.

An yanka manyan raguna biyu kamar yadda ya ke a sunnar babbar sallah domin yin shagali.

Bayan hakan, Shugaban kasar da iyalansa sun dauki hotuna wadda daga bisani aka wallafa su dandalin sada zumunta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel