Ta'addanci: Ya kamata Buhari ya san barnar da dakarun sojoji suke yi - Gwamna Zulum zai fasa kwai

Ta'addanci: Ya kamata Buhari ya san barnar da dakarun sojoji suke yi - Gwamna Zulum zai fasa kwai

- Gwamna Zulum ya ce akwai bukatar Shugaban kasa Buhari ya san gaskiyar cewa akwai wasu makirai da ke aiki ta karkashin kasa domin wahalar da kokarin gwamnati na hana ta’addanci

- Zulum ya bukaci Shugaban Najeriyan da ya duba tsarin tsaron kasar da kyau domin tabbatar da nasara a kan ‘yan ta’addan

- Gwamnan na ta zafafan kalamai tun bayan da ‘yan bindiga suka kai wa ayarin motocinsa hari ‘yan kwanaki da suka gabata

Gwamnan jihar Borno, Babagan Zulum, ya yi ikirarin cewa lallai akwai masu barna da gangan da ke aiki domin hana kawo karshen yaki da Boko Haram a Najeriya.

Channels TV ta ruwaito cewa Zulum ya yi zargin ne a Borno a ranar Lahadi, 2 ga watan Agusta, lokacin da ya hadu da takwarorinsa na jihar Kebbi, Atiku Bagudu da na jihar Jigawa, Badaru Abubakar.

Zulum ya ce ya yarda akwai wasu runduna da ke aiki domin hana gwamnati kawo karshen ta’addanci a yankin arewa maso gabas.

Ta'addanci: Ya kamata Buhari ya san barnar da dakarun sojoji suke yi - Gwamna Zulum zai fasa kwai
Ta'addanci: Ya kamata Buhari ya san barnar da dakarun sojoji suke yi - Gwamna Zulum zai fasa kwai Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Gwamnonin arewan biyu sun kai masa ziyara ne biyo bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai wa jerin motocinsa kwanan nan.

KU KARANTA KUMA: Sanata Ndume ya goyi bayan samun shugaban kasa daga kudu a 2023

Taron ya kuma samu halartan tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima, Sanata Ali Ndume da mambobin majalisar dokokin jihar.

Gwamna Zulum ya ce akwai bukatar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya duba tsarin tsaron kasar da kyau domin tabbatar da ganin cewa kokarinsa bai tashi a banza ba.

A baya mun ji cewa Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Elkanemi, ya yi korafin cewa daga yanzu jihar Borno bata tsira ba.

Ya fadi hakan ne biyo bayan harin kwanan nan da aka kai wa ayarin motar Gwamna Babagana Zulum, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A ranar Laraba ne ‘yan ta’adda suka kai wa jerin motocin gwamnan farmaki a garin Baga da ke karamar hukumar Kukawa na jihar yayin wata ziyara.

Da yake magana a lokacin gaisuwar Sallah da ya kai gidan gwamnati a Maiduguri, Shehu ya ce: “Ya mai girma, bamu ji dadin abunda ya faru ba a Baga, abun bakin ciki ne da kaico. “

Idan har za a iya kai wa ayarin motocin shugaban tsaro guda hari, toh wallahi, babu wanda ya tsira saboda shine mutum na daya a jihar.

“Idan har za a iya kai wa ayarin motocin irin wannan mutum mai daraja hari, na maimaita; babu wanda ya tsira. Lamarin na kara tabarbarewa, ina bukatar kowa da ya tashi mu hada hannu domin neman Allah ya shiga lamarin."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel