Tsohon Shugaban PDP na kasa ya sauya sheka zuwa APC

Tsohon Shugaban PDP na kasa ya sauya sheka zuwa APC

- Cif Barnabas Gemade, tsohon shugaban jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) na kasa ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC)

- Gemade wanda ya ce komawarsa APC tamkar komawa gida ne ya sauya shekar ne tare da dubban magoya bayansa

- Jam'iyyar APC ta yi farin ciki da wannan babban kamu da ta yi

Tsohon shugaban jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) na kasa, Cif Barnabas Gemade ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), bayan batawa da jam’iyyar Social Democratic Party (SDP).

Dubban magoya bayansa sun bi shi zuwa APC a unguwarsa da ke yankin Mbawar, karamar hukumar Konshisha da ke jihar Benue.

Ya ce ya yanke shawarar komawa APC ne bayan duba yanayin siyasarsa da ta jihar Benue, inda ya ce komawarsa APC ya kasance tamkar komawa gida ne.

Gemade ya wakilci yankin Benue ta arewa maso gabas a majalisar dattawa karkashin jam’iyyar APC daga 2015 zuwa 2019, jaridar The Nation ta ruwaito.

Ya mika godiya ga shugabannin APC, ciki harda Shugaban kasa Muhammadu Buhari, mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni.

Ya kuma jinjinawa ministan ayyuka na musamman, Sanata George Akume, inda ya nuna kudirinsa na aiki domin gyara jam’iyyar a jihar domin ta kara karfi.

Tsohon Shugaban PDP na kasa ya sauya sheka zuwa APC
Tsohon Shugaban PDP na kasa ya sauya sheka zuwa APC Hoto: The Nation
Asali: UGC

Gemade ya ce hada kai da suka yi tare da Akume, tun bayan dawowar siyasar jam’iyya a 1999, yana kawo nasarar zabe a jihar.

Shugaban APC a Benue, Kwamrad Abba Yaro ya tarbi Gemade a madadin jam’iyyar.

Ya ce ya kasance rana mai matukar muhimmanci ga APC saboda Cif Gemade ya kasance babban kifi.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo: Obaseki ya hadu da babban cikas yayinda ‘yan uwansa 2 suka koma bayan Ize-Iyamu

“Bamu ji dadi ba a lokacin da ka tafi. Yanzu da ka dawo muna farin ciki. Rana ce mai kyau ga APC saboda Cif Gemade ya kasance babban kifi.

“Bari na baka tabbacin cewa babu sabuwar APC ko tsohuwar APC, ana daukar kowa daya ne kuma duk muna da yancin iri guda ne.

“Mu yan uwan juna ne. Don haka, mu marawa junanmu baya sannan mu yi aiki a matsayin tawaga daya.

“Idan sakatariyar jam’iyyar a jihar ta yi maka laifi ta kowani fanni, ka yafe mana,” in ji Yaro.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel