Zaben Edo: Obaseki ya hadu da babban cikas yayinda ‘yan uwansa 2 suka koma bayan Ize-Iyamu
- Wasu ‘yan uwan Gwamna Obaseki sun zabi hada kai da babban dan adawarsa, Osagie Ize-Iyamu
- ‘Yan uwan gwamnan masu suna Osaro da intor sun ce za su mara wad an takarar APC baya a zaben mai zuwa
- A nashi bangaren, Ize-Iyamu ya cika da farin ciki kan goyon bayan da ya samu daga ‘yan uwan Obaseki
Gwamna Godwin Obaseki ya rasa goyon bayan wasu ‘yan uwansa biyu gabannin zaben gwamnan jihar Edo.
Mazajen biyu masu suna Osaro Obaseki da Victor Obaseki sun kasance makusantan gwamnan na jihar Edo.
Sun zabi goyon bayan babban abokin adawar gwamnan, Fasto Osagie Ize-Iyamu, wanda yake dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), PM News ta ruwaito.
A wajen wani taro tare da Ize-Iyamu a Benin, Victor ya ce su ahlin Obaseki mutane ne na daban da ke abubuwansu ta hanyoyi na musamman.
A cewarsa, koda dai Obaseki ne nasu, Ize-Iyamu za su mara wa baya.
“Ina mara masa baya a chan baya, kuma zan ci gaba da goyon bayansa, za mu yi dukkanin kamfen dinmu ba tare da matsala ba, daga kasar zuciyarmu,” in ji shi.
Da yake martani ga wannan karamci nasu, Ize-Iyamu na nuna farin ciki. Ya bayyana matakin ‘yan uwan abokin adawar nasa a matsayin tabbacin cewa babu ci gaba a jihar Edo a shekaru hudu da Obaseki ya kwashe kan mulki.
Ya ce: “Bari na gode maku kan goyon bayan. Na san wasun ku tun shekaru da dama da suka gabata kuma ina farin cikin cewa siyasa bai shafi alakarmu ba.”
KU KARANTA KUMA: Rashin Tsaro: Dalilin da ya sa babu wanda zai tsira a Najeriya - Shehun Borno
Ize-Iyamu ya wallafa a shafinsa na twitter cewa: “A safiyar yau, na samu goyon bayan manyan ahlin Obaseki a wani taro karkashin jagorancin Mista Osaro da Victor Obaseki.
“Kamar hadiman gwamnan da manyan masu mukamai, ‘yan uwansa sun yarda cewar ya gaza wa mutanen Edo kuma bai cancanci zarcewa ba.”
A ranar 19 ga watan Satumba, mutanen jihar Edo za su fito kwansu da kwarkwatansu domin zabar sabon shugaba.
Obaseki zai yi takara a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) bayan tsohuwar jam’iyyarsa ta APC ta hana shi tikiti.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng