Rashin Tsaro: Dalilin da ya sa babu wanda zai tsira a Najeriya - Shehun Borno

Rashin Tsaro: Dalilin da ya sa babu wanda zai tsira a Najeriya - Shehun Borno

- Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Elkanemi ya yi martani a kan halin rashin tsaro a kasar musamman jiharsa

- Ya ce daga yanzu babu wanda zai tsira a jihar tunda har aka iya kai wa ayarin motocin shugaban tsaro na jihar hari

- Basaraken ya yi sharhi ne a kan harin da wasu 'yan ta'adda suka kai wa motoci Gwamna Babagana Zulum

Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Elkanemi, ya yi korafin cewa daga yanzu jihar Borno bata tsira ba.

Ya fadi hakan ne biyo bayan harin kwanan nan da aka kai wa ayarin motar Gwamna Babagana Zulum, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A ranar Laraba ne ‘yan ta’adda suka kai wa jerin motocin gwamnan farmaki a garin Baga da ke karamar hukumar Kukawa na jihar yayin wata ziyara.

Rashin Tsaro: Dalilin da ya sa babu wanda zai tsira a Najeriya - Shehun Borno
Rashin Tsaro: Dalilin da ya sa babu wanda zai tsira a Najeriya - Shehun Borno Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Da yake magana a lokacin gaisuwar Sallah da ya kai gidan gwamnati a Maiduguri, Shehu ya ce: “Ya mai girma, bamu ji dadin abunda ya faru ba a Baga, abun bakin ciki ne da kaico.

“Idan har za a iya kai wa ayarin motocin shugaban tsaro guda hari, toh wallahi, babu wanda ya tsira saboda shine mutum na daya a jihar.

“Idan har za a iya kai wa ayarin motocin irin wannan mutum mai daraja hari, na maimaita; babu wanda ya tsira. Lamarin na kara tabarbarewa, ina bukatar kowa da ya tashi mu hada hannu domin neman Allah ya shiga lamarin."

Gwamna Zulum ya yi godiya ga Shehu a kan ziyarar sannan ya bashi tabbaci a kan shirin gwamnati na magance lamarin da ya gabatar.

Biyo bayan hare-haren kwanan nan da Boko Haram suka kai a jihar Borno da wanda aka kai kan ayarin motocin gwamnan, masu hasashe da manyan masu ruwa da tsaki sun yi kira ga sake lamarin tsaron kasar, ciki harda tsige shugabannin tsaron kasar.

Wani tsohon jigon rundunar soji na jihar Benue, Kanal Aminu Isa Kontagora (mai ritaya), ya kuma bukaci rundunar soji da ta binciki zargin Gwamna Babagana Zulum na cewa akwai masu barna da gangan cikin rundunar sojin.

KU KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun kama saurayin da ya yi wa 'yar shekara 2 fyade

Kakakin rundunar soji, Kanal Sagir Musa, ya ce tuni rundunar soji ta fara bincike a kan lamarin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng