Rashawa: Buhari ya bayyana yadda wasu makusantansa suka ci amanarsa

Rashawa: Buhari ya bayyana yadda wasu makusantansa suka ci amanarsa

A ranar Juma'a a fadar shugaban kasa da ke Abuja, shugaban kasa Muhammadu Buhari a karon farko ya yi magana a kan zargin cin rashawa da ake zargin wasu shugabannin cibiyoyin gwamnatin tarayya da hukumomi.

Wadannan hukumomin sun hada da hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da kuma hukumar kula da ci gaban yankin Neja Delta.

Shugaban kasar wanda ya yi jawabin bayan kammala sallar idi a gaban fadar shugaban kasa, ya ce wasu manyan masu mukami na gwamnati a karkashin mulkinsa da wanda ya gabata sun ci amanarsa.

Ya nuna jin dadinsa da yawa aka samo wasu kadarorin kasar nan da aka sace kuma aka siyar, amma yanzu an saka su a tsarin asusu na bai daya (TSA), wanda ba zai yuwa mahandama su taba ba.

A yayin da aka tambayesa yadda ya ji game da tone-tonen da ke fitowa da EFCC da NDDC, Buhari ya ce:

"Akwai cin amana da wasu wadanda na yarda da su na gwamnatina da wacce ta shude suke yi. An samo wasu kadarori da wasu kudade.

"Amma mun kirkiro tsarin asusun bai daya (TSA), wanda dukkan kudin da aka samo ake zubawa ta yadda za a dinga duba shi babu mai iya taba wa."

Rashawa: Buhari ya bayyana yadda wasu makusantansa suka ci amanarsa
Rashawa: Buhari ya bayyana yadda wasu makusantansa suka ci amanarsa. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Boko haram: Zulum ya bayyana mataki mai tsauri da zai dauka

Yayin tabbatar wa da dukkan wadanda ake bincika na da da na yanzu cewa za a ci gaba, ya ce: "Wannan ne yasa muke tsananta bincikar dukkan hukumomin."

Ya jaddada cewa dukkan wadanda ake zargin za a bankadosu kuma za a hukunta su, wanda gwamnatinsa ne za ta yi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, majalisar dattawa da ta wakilai na bincikar kwamitin rikon kwarya na hukumar kula da yankin Neja Delta a kan watanda da wasoso da suka yi da N40 biliyan na hukumar.

Kamfanin Dillancin Labaran ya ruwaito cewa, kwamiti a fadar shugaban kasa wanda ke samun shugabancin Jastis Ayo Salami na bincikar zargin almundahana da ake wa shugaban EFCC, Ibrahim Magu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel