Labari mai zafi: Wasu bama-bamai sun fashe a babban birnin Maiduguri

Labari mai zafi: Wasu bama-bamai sun fashe a babban birnin Maiduguri

- Bama-bamai biyu sun tashi da yammacin Ranar Alhamis a Maiduguri

- An kai wannan hari ne a wasu wurare biyu da aka yi sanadiyyar rayuka

- ‘Yan Sanda sun tabbatar da wannan bayan an kai wa Gwamna hari jiya

Labarin da mu ke samu daga jaridar The Cable shi ne wasu bama-bamai sun fashe a garin Maiduguri, jihar Borno.

Bam biyu aka ji tashinsu a babban birnin na jihar Borno a yammacin ranar Alhamis, 30 ga watan Yuli, 2020.

Rahoton ya bayyana cewa wadannan bama-bamai sun tashi ne a mabanbantan lokaci, mintuna kusan goma aka shafe tsakaninsu.

Jaridar ta ce bam din fari ya tashi ne a unguwar Gunge da kimanin karfe 6:00 na yamma.

Dayan bam din ya buga ne a wani wurin saida motoci da ke cikin babban birnin na jihar Borno, ‘yan mintuna bayan tashin bam din farko.

KU KARANTA: Boko Haram ta yankewa Sojojinta hukuncin kisa

Channels TV ta fitar da rahoto cewa akalla mutane biyar wannan ta’adi ya hallaka.

Kwamishinan ‘Yan sanda na jihar Borno, Mohammed Ndatsu, ya shaidawa manema labarai aukuwar wannan mummunan lamari.

Jami’in ‘yan sandan ya tabbatar da cewa kungiyar Boko Haram ne ta kai wannan hari a jihar ta Arewa maso gabas, kuma an rasa mutane biyar.

Idan ba ku manta ba a ranar Laraba ne wasu ‘yan ta’addan Boko Haram su ka kai wa tawagar gwamna Babagana Zulum hari a karamar hukumar Kukawa.

Kawo yanzu ‘Yan Boko Haram ba su tabbatar da cewa su ne su ka kai wannan hari ba. Har yanzu ana fama da harin ‘yan ta’adda a Borno.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel