Godwin Obla: Saboda na bukaci kudin aikina N762m, Ibrahim Magu ya sa aka tsare ni

Godwin Obla: Saboda na bukaci kudin aikina N762m, Ibrahim Magu ya sa aka tsare ni

Tsohon lauyan hukumar EFCC, Godwin Obla SAN ya ce tsohon shugaban hukumar da aka dakatar, Ibrahim Magu, ya hana shi kudin aiki da ya yi har Naira miliyan 763.9m.

Cif Godwin Obla ya bayyana cewa da ya huro wuta a kan a biya shi kudinsa, sai Ibrahim Magu ya bada umarni a rufe shi, ya kuma bada umarnin a kama shi da laifin ba Alkali rashawa.

Babban lauya ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya bayyana gaban kwamitin shugaban kasa da ke binciken EFCC, wanda tsohon Alkali mai shari’a, Ayo Salami ya ke jagoranta.

Lauyan ya gabatar da wasika mai taken: “‘Presentation In Respect of Malicious and Reckless Abuse of State Power of Investigation and Prosecution Resulting in Mismanagement of Forfeited Assets by Deliberate and Contrived Incompetence and Suspicious Dealing of Forfeited Assets.”

A wannan takarda mai tsawon shafuka 18, Obla ya zargi Magu da rashin sanin aiki da ganganci, wuce gona da iri, da kuma facaka da kudin da EFCC ta karbo daga hannun barayin kasa.

Rahoton ya ce Godwin Obla ya bayyana ne a gaban wannan kwamiti da ke aiki a fadar shugaban kasa, kuma a gaban Ibrahim Magu, har ya jefawa tsohon shugaban na EFCC wasu tambayoyi.

KU KARANTA: Magu bai ba mataimakin shugaban kasa kudi ba

Godwin Obla: Saboda na bukaci kudin aikina N762m, Ibrahim Magu ya sa aka tsare ni
Ibrahim Magu Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Obla ya mika wasu tambayoyi 12 da ya fadawa kwamitin ya kamata shugaban na EFCC da aka dakatar ya amsa su, ya kuma bada shawarwari biyar da za a bi domin gyara hukumar.

Bayan haka, Obla ya mika hujjoji fiye da 10 a gaban kwamitin, daga ciki har da takardun ladan aikin da ya yi wa hukumar. Ya ce ya tsayawa EFCC a shari’a 40 a gaban Alkali.

Kamar yadda Lauyan ya fada, daga cikin shari’ar da ya yi wa EFCC nasara a kotu, akwai karar hukumar da CBN a karkashin Lamido Sanusi, wanda shari’ar ta kawowa EFCC makudan kudi.

A lokacin da Lauyan ya nemi a biya shi kudin aikinsa, sai aka fara kai da korafi a kansa. “A dalilin haka Magu da gangan ya ana ni ladar gumi na, ya maka ni a kotu a kan zargin soki-burutsu.”

Cif Obla ya ke cewa Magu ya zarge shi da bada rashawa ga Alkali Rita Ofili-Ajumogobia, zargin da ya karyata.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel