Bidiyon harin da 'yan Boko Haram su ka kaiwa tawagar gwamna Zulum a Borno

Bidiyon harin da 'yan Boko Haram su ka kaiwa tawagar gwamna Zulum a Borno

A jiya, Laraba, ne Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa an kai wa tawagar gwamna Babagana Zulum na jihar Borno hari a garin Baga da ke jihar Borno a ranar Laraba 29 ga watan Yulin shekarar 2020.

Wata majiya a rundunar tsaro ta shaidawa The Cable cewa gwamnan yana kan hanyarsa ta zuwa sansanin yan gudun hijira da ke jihar ne a lokacin da abin ya faru.

"Gwamnan ya tafi Kukawa, kuma yana kan hanyarsa ta zuwa Baga ne aka kai masa hari. Babu wanda ya jikkata," a cewar majiyar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa Zulum ya koma Maiduguri, babban birnin jihar misalin karfe 9.10 na daren ranar Laraba.

Kalli bidiyon harin:

Wani Mohammed Mai Bukar, daya daga cikin hadiman gwamnan ya tabbatar wa alummar garin cewa babu abinda ya sami gwamnan.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Bukar ya rubuta, "Ga mazauna jiharmu, Mai girma Farfesa Zulum da tawagarsa suna nan lafiya kuma babu wanda ya mutu. Mun gode."

Wannan shine karo na biyu da ake kai wa tawagar Gwamna Zulum hari cikin shekara guda.

A yayin da gwamnan ke dawowa daga wata tafiya daga karamar hukumar Baga a bara, an kai wa tawagarsa hari a Konduga duk dai a jihar ta Borno.

Harin ya faru ne watanni bakwai bayan da yan taada suka kai wa tawagar Kashim Shettima tsohon gwamnan jihar hari a hanyarsa ta zuwa Gamboru Ngala duk dai a jihar Borno.

A kalla mutane 60 suka riga mu gidan gaskiya a wancan harin kuma aka sace kimanin mutane 100.

Bidiyon harin da 'yan Boko Haram su ka kaiwa tawagar gwamna Zulum a Borno
Zulum da Buratai a jihar Borno
Asali: Facebook

An yi kokarin ji ta bakin mai magana da yawun gwamnan, Isa Gusau da Kwamishinan Labarai na jihar Borno, Babakura Abba-Jatto don karin bayani amma ba su amsa sakon kar ta kwana ba kuma ba su daga wayarsu ba.

Farfesa Zulum, a ranar Laraba, ya nuna bacin ransa a kan yanayin aikin dakarun sojin da ke kokarin ganin bayan 'yan ta'addan Boko Haram a garin Baga da ke karamar hukumar Kukawa ta jihar.

DUBA WANNAN: Tubabben dan Boko Haram da gwamnati ta saki ya kashe mahaifinsa ya kwashi dukiya ya gudu

Ya nuna fushinsa a kan harin da wasu da ake zargin 'yan ta'addan Boko Haram ne suka kai masa a hanyarsa ta fita daga Baga.

Baga gari ne da ke da nisan a kalla kilomita 196 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Gwamnan ya matukar fusata da lamarin, ganin cewa akwai dakarun sojin masu tarin yawa a nisan da bai wuce mil 4 ba wanda daidai yake da kilomita 4 daga Baga, amma basu iya kwace garin ba.

Zulum ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da sake bude babbar hanyar Monguno zuwa Baga ga ababen hawa wacce aka yi shekaru biyu da rufewa.

"Sama da shekara daya kuna nan, akwai soji 1,181 a nan. Idan ba za ku iya karbar Baga ba wacce take da nisan da bai kai kilomita biyar ba daga inda kuke, toh me kuke yi?," Zulum ya tambayi sojojin a fusace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel