Gwamnatin Tarayya za ta biya kason N8.6bn a yarjejeniyar aikin Siemens - FEC

Gwamnatin Tarayya za ta biya kason N8.6bn a yarjejeniyar aikin Siemens - FEC

A wajen taron FEC na majalisar zartarwa ta Najeriya da aka yi a jiya, 29 ga watan Yuli, 2020, an amince da fitar da kudin da za a biya kamfanin Siemens domin aikin wutar lantarki.

FEC ta amince a saki fam miliyan €15.21 (Naira biliyan 6.94) da wasu Naira biliyan 1.708 da nufin gwamnatin Najeriya ta biya kasonta a yarjejeniyar da aka shiga da kamfanin Siemens.

Gwamnatin tarayya ta shiga yarjejeniyar lantarkin ne da Siemens AG na kasar Jamus a shekarar 2019.

Ministar tattalin arziki da kasafin kudi, Zainab Ahmed, ta shaidawa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa ita da ministan wuta, Saleh Mamman sun kawo maganar gaban FEC.

Punch ta ce a Disamban bara gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ware Naira biliyan 61 domin aikin samar da wutar lantarki wanda wannan kamfani na kasar waje zai yi.

Bayan gabatar da wannan takarda a taron ministocin da aka yi ranar Laraba, majalisar ta yarda a soma fitar da wannan kudi N8, 648, 081, 465.2 domin a fara aikin inganta lantarkin kasar.

KU KARANTA: Najeriya za ta karbi wasu kudi daga kasashen waje - AGF

Gwamnatin Tarayya za ta biya kason N8.6bn a yarjejeniyar aikin Siemens - FEC
Ministar kudi Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Ana sa ran Najeriya za ta kashe Biliyan €3.11 ko kuma Naira tiriliyan 1.15 a wasu manyan jihohi hudu. Idan an kammala aikin za a samu karin megawatts 25, 000 na karfin lantarki.

Daga cikin ayyukan da wannan yarjejeniya ta kunsa akwai kwangilar wutan na ruwan Mambilla wamda aka warewa Naira biliyan biyu, aikin 2x60MVA 132/33kV da ke Gwaram, Jigawa.

Har ila yau kwangilar za ta shafi aikin 215MW a Kaduna da Kashambilla, jihar Taraba. Tashoshin nan uku da ke Jigawa, Kaduna da Taraba za su ci kusan Naira tiriliyan 1.5

Ministar tattalin arziki da kasafi, Zainab Ahmed ta ce kwangilar da za a fara za ta kunshi ayyuka 23 na jawo wutan lantaki da wasu ayyuka 175 dabam. Za a kammala aikin a 2025.

“Kwangilar zai kuma taimakawa hukumar NERC wajen inganta harkar amfani da na’ura wajen auna wutar lantarkin da mutane su ke sha.” a cewar Ahmed.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel